Hukumar tsaro ta DSS a Nijeriya ta saki AbdulRasheed Bawa, tsohon shugaban hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa.
An saki tsohon shugaban EFCC ne ranar Laraba fiye da wata hudu bayan DSS ta kama shi, kamar yadda sanarwar da kakakin hukumar Peter Afunanya, ya wallafa a shafinsu na X ta bayyana.
"DSS ta tabbatar da sakin tsohon shugaban EFCC, AbdulRasheed Bawa, awanni kadan da suka gabata (a yau, 25 ga watan Oktoba, 2023)," in ji sanarwar.
Sai dai sanarwar ba ta yi karin bayani game da sakin nasa ba.
Wasu bidiyoyi da aka rika watsawa a shafukan sada zumunta sun nuna Bawa a gida tare da iyalansa ana cike da murna.
Labari mai alaka: AbdulRasheed Bawa ya shiga hannun DSS bayan an dakatar da shi daga EFCC
A watan Yunin da ya gabata ne DSS ta "gayyaci" AbdulRasheed Bawa "don binciken da ake yi da ya shafe shi" jim kadan bayan shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya dakatar da shi daga kan mukaminsa.
"Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da dakatar da Mr. AbdulRasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) domin samun damar gudanar da binciken da ya dace kan ayyukan da ya yi lokacin da yake rike da ofishinsa," in ji sanarwar da Willie Bassey, daraktan watsa labarai na Sakataren Gwamnatin ya fitar a wancan lokacin.
An dauki matakin ne bayan manyan zarge-zargen da ake yi masa na amfani da ofishinsa ba bisa ka'ida ba, a cewar sanarwar.
A shekarar 2021 gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta nada AbdulRasheed Bawa a matsayin shugaban EFCC wanda ya maye gurbin Umar Mohammed Abba, mutumin da ya rike mukamin shugaban riko na hukumar.