Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Nijeriya DSS ta musanta zarge-zargen da ake yi kan cewa babban daraktan hukumar Magaji Yusuf Bichi ya yi sama da fadi da kudin tallafi na ma’aikatan hukumar.
Mai magana da yawun hukumar Peter Afunanya ne ya fitar da sanarwar inda ya musanta zargin da wani Jackson Ude ya yi a shafin X wanda ya yi zargin shugaban DSS din da kwashe kudin.
Afunanya ya tabbatar da cewa babu wasu kudi da aka bai wa hukumar a halin yanzu domin ma’aikata kuma da zarar an fitar da wadannan kudade za a bai wa ma’aikatan hakkinsu.
“Hukumar tana son sanar da cewa zarge-zargen da ake yi ba gaskiya bane. Hukumar na son tabbatar da cewa daraktan hukumar ko wani mai aiki da umarnin shi, babu a cikinsu wanda ya sace kudin tallafin da aka bai wa ma’aikata.
“Babu wani tallafi da aka bai wa hukumar kuma da zarar an bayar da shi, za a bai wa ma’aikatan hakkinsu,” in ji sanarwar.
Hukumar ta DSS ta bukaci jama’a su yi watsi da karerayin da ake yadawa wadanda ke kawo rabuwar kai da kuma rikici.
Haka kuma hukumar ta tabbatar da cewa daraktan na DSS zai dauki matakai na shari’a dangane da lamarin.