Dan Afirka ta Kudu, Johann Rupert, ya sha gaban attajirin Nijeriya, Aliko Dangote, a matsayin wanda ya fi kudi a nahiyar Afirka.
Sabon jadawalin attajiran da suka fi arziki a duniya da mujallar Forbes ta fitar ya nuna cewa Dangote ya sauko daga matsayin ne bayan dala biliyan $3.8bn sun ragu daga cikin arzikinsa.
Mujallar ta ce arzikin Dangote ya koma dala biliyan $9.7 a watan Janairun shekarar 2024, yayin da arzikin Johann Rupert dan kasar Afirka ta Kudu ya koma dala biliyan 10 a cikin watan Janairun shekarar 2024.
Duk da cewar shi ma attajirin Afirka ta Kudun ya rasa dala miliyan $700m cikin arzikin nasa, shi ne ya fi arziki a nahiyar Afirka, in ji mujallar ta Forbes.
Johann Rupert mai shekara 73 dai shi ne shugaban kamfanin kayan alatu na Compagnie Fiannciere Richemonte da ke kasar Switzerland.

Kazalika Abdul Samad Rabiu, shugaban kamfanin BUA, ya koma attajiri na shida da ya fi kudi a Afirka daga matsayi na hudu da yake a baya, in ji mujallar Forbes.
Shi kuma Mike Adenuga, shugaban kamfanin Globacom, ya koma na 10 daga matsayi na shida a jerin attajiran da suka fi kudi a Afirka.
Ana ganin karyewar darajar naira da darajar kudin Rand na Afirka ta Kudu ya taka rawa wajen rage yawan arzikin attajiran na Afirka a rahoton mujallar Forbes.