Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA) ta yi ƙarin haske kan dalilan da suka sa ƙasar ta rasa matsayin aji ɗaya da ake buƙata wanda ya yi sanadiyar haramta wa kamfanonin jiragen sama na Nijeriya shiga Amurka.
Dole Nijeriya ta samu matsayi na ɗaya wato ''Category 1 Status'' don iya zirga-zirga a Amurka kamar sauran kasashe a shirin duba lafiyar jiragen sama na duniya wato (IASA), a cewar wata sanarwa da Hukumar ta NCAA ta fitar a shafinta na X da ke ɗauke da sa hannun mukaddashin Darakta Janar na Hukumar, Kyaftin Chris Najomo a ranar Talata.
“An sake jawo hankalin hukumar NCAA kan wani labari da ke yawo a kafafen intanet game da zargin cewa Amurka ta haramta wa kamfanonin jiragen sama na Nijeriya sauƙa a ƙasar.
''Saboda mummunar fahimtar da irin wannan labarai kan iya haifawar, ya zama wajibi mu yi ƙarin haske yadda ya kamata.'' in ji sanarwar NCAA.
''Bayan ƙasa ta samu matsayin aji na ɗaya, za a bai wa kamfanonin jiragen saman Nijeriya izinin zirga-zirga da jiragen da aka yi wa rajista da sauran kananan jiragen haya da aka musu rajistar shiga Amurka, a ƙarkashin yarjejeniyar haɗin gwiwar jiragen sama da aka ƙulla ta (BASA)," in ji shugaban a cikin sanarwar.
Hukumar ta NCAA ta ce Nijeriya ta samu matsayin aji na ɗaya a karon farko ne a watan Agustan shekarar 2010, yayin da hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta Amurka (FAA) ta sake gudanar da wani aikin tantance lafiyar jiragen Nijeriya a shekarar 2014.
Najomo ya bayyana cewa an sake gudanar da aikin tantance lafiyar jiragen Nijeriya a shekarar 2017, inda daga nan ƙasar ta ci gaba da riƙe matsayinta a aji ɗaya.
Shugaban na NCAA ya ce, daga watan Satumba na 2022, Hukumar FAA ta Amurka ta soke jerin kasashe masu matsayin aji ɗaya, waɗanda bayan shekaru biyu, ba su da wani kamfani da zai yi aiki a Amurka ko kuma wanda ke ɗauke da lambar izinin jirgin sama na aiki a Amurka.
''Kazalika sauran ƙasashen da aka cire su daga jerin masu matsayin aji ɗaya har da waɗanda hukumar FAA ba ta bai wa taimakon fasaha bisa ga rashin bin ƙa'idojin ƙasa da ƙasa kan tsaro da aka gano.
“Babu wani kamfani daga Nijeriya da ya je a Amurka ta hanyar amfani da wani jirgin Nijeriya da aka yi wa rajista da a tsakanin skekaru biyu kafin watan Satumba na 2022.
''Don haka, dama an yi hasashen za a cire Nigeriya kamar yadda aka yi wa wasu ƙasashe da suka fada cikin wannan rukuni, saboda haka tun daga 2022 aka cire ƙasar kuma an sanar da ita kan wannan mataki a tun a shekarar, ”in ji shi majomo.
Ya ƙara da cewa soke matsayin Nijeriya ba shi da wata alaka da duk wani rashin aminci ko rashin tsarin sa ido na tsaro na kasar.