Ana yawan sace daliban Jami'ar Tarayya ta Lafia. Hoto: Federal University of Lafia website

Daliban Jami’ar Tarayya ta Lafia da ke Jihar Nasarawa a yankin arewa ta tsakiyar Nijeriya sun yi zanga-zangar sace mutum 10 da aka yi daga makarantarsu.

Daliban wadanda suka yi zanga-zangar a ranar Alhamis dauke da kwalaye masu rubuce-rubucen neman a ceto abokan karatun nasu, sun bukaci hukumomi da su dakatar da yawan sace su da ake yi a makarantar.

“Iyayenmu ba za su iya ci gaba da biyan kudin fansa ba, kuma satar mutane barazana ce ga ilimin ‘ya’ya mata,” suka yi ta ihun fada a lokacin zanga-zangar, wacce jami’an tsaro suka yo ta kokarin hana su ta hanyar fesa hayaki mai sa hawaye, saboda tare hanya da suka yi, kamar yadda gidan rediyon tarayyar Nijeriya FRCN ya rawaito.

Da yake magana kan abin da ya sa aka yi amfani da hayaki mai sa hawaye don hana zanga-zangar, mukaddashin kwamishinan ‘yan sandan Jihar Nasarawa, DCP Shettima Muhammed ya ce bai kamata daliban su tare hanya ba.

“Haramun ne a toshe babbar hanya tare da hana ‘yan kasa da ba su ji ba, ba su gani ba amfani da titin, matafiya da ke bin hanyar Lafiya zuwa Jihar Binuwai da sauran sassan kasar sun kasa iya wucewa.

“Dole sai da muka tura jami’ai don tarwatsa daliban. Suna da hakkin yin zanga-zanga amma ban da toshe hanya,” kamar yadda ya fada.

Kwamishinan ‘yan sandan ya kara da cewa an tsaurara tsaro a kewayen jami'ar ta hanyar zuba karin jami’an tsaro masu siniri.

Shi ma shugaban sashen hulda da jam’a na Jami’ar Tarayya ta Lafia Ibrahim Abubakar, ya yi kira ga dalibai da su kwantar da hankulansu, yana mai cewa hukumar makarantar ta karfafa hadin gwiwa da hukumomin tsaro don kare yankin.

Yawan satar dalibai

Daliban jami’ar sun ce sun yi zanga-zangar ne saboda sun kai makura kan yadda ake yawan sace dalibai a makarantar da kewayenta, inda a ranar Laraba aka sace dalibai na baya-bayan nan kusan 10.

Kauyen Gandu shi ne wanda ya fi kusa da jami’ar tun bayan kafa ta a shekarar 2012, kuma mazauna wajen sun ce a shekarar nan ta 2023 satar mutane da sauran miyagun laifuka sun ta’azzara sosai a yankin.

Hakan ne ya sa bayan satar daliban na ranar Laraba, sai daliban jami'ar da al’ummar kauyen Gandun suka hadu wajen yin zanga-zangar tare da tare babban titin Lafia zuwa Makurdi, lamarin da ya jawo cunkoson ababen hawa.

Maigarin kauyen Gandu Mallam Hassan Kassimu na daga cikin wadanda suka shiga cikin zanga-zangar daliban, inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Nasarawa da su dauki kwakkwaran mataki don dakile rashin tsaron.

A watan Oktoban da ya gabata ma an sace wasu dalibai shida daga Jami’ar Tarayya ta Lafia, inda har sai da iyayensu suka biya naira miliyan biyar a matsayin kudin fansa kafin barayin su sake su, kamar yadda rahotanni suka ce.

TRT Afrika da abokan hulda