Daga N'Djamena, dakarun Faransa za su bar ƙasar ta jirgin sama da muhimman kayan aikinsu. Hoto: Reuters

Chadi ta ce sojojinta za su yi wa dakarun Faransa rakiya wadanda makwabciyarta Nijar ta kora yayin da suka kama hanyar koma gida Faransa, kamar da yadda gwamnatin mulkin sojin Nijar ta bukata.

Dakarun Faransa za su mayar da kayayyakin aikinsu ta kasa a cikin kasar Chadi da Kamaru – tafiya ce ta fiye da kilomita 3,000 (kimanin mil 1,860) wani wuri ne da ke ɓoye ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi.

"Chadi ta amince ta bayar da hanya a cikin ƙasarta wajen komawar dakarun Faransa koma wa ƙasarsu," kamar yadda babban hafsan sojin Chadi Abakar Abdelkerim Daoud ya ce a wata sanarwa a ranar Alhamis.

"Dakarun Chadi za su raka ayarin [dakarun Faransa] daga iyakar kasar Nijar zuwa birnin N'Djamena kafin su ƙarasa filin jirgin sama… da kuma zuwa iyakar Kamaru zuwa birnin Douala."

Akwai akalla sojoji 1,400 da ke zaune a birnin Yamai da kuma yammacin Nijar wadanda suke yaki da Kungiyar IS da Al-Qaeda, inda suke da tarin kayan aiki.

Ayarin farko sun taso ne daga sansaninsu a Quallam zuwa Chadi mai maƙwabtaka a ranar Talata, inda suke tafiya ta hanyar mota a motoci masu sulke bisa rakiyar dakarun Nijar a tafiyar da ta kai kilomita 1,600.

Daga N'Djamena, dakarun Faransa za su bar ƙasar ta jirgin sama da muhimman kayan aikinsu.

Za a wuce da muhimman kaya ta ƙasa da ruwa, in ji wani tsohon sojan Faransa a Afirka wanda ya buƙaci a sakaya sunansa.

An rufe iyakar Nijar da Benin da Nijeriya tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Shugaba Bazoum ranar 26 ga watan Yulin.

AFP