CAF ta ce za ta ɗauki mataki kan duk wanda ya saɓa dokokinta. / Hoto: CAF

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ta ƙaddamar da bincike kan abin da ya sa tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya ta ƙi buga wasan neman shiga gasar AFCON da Libya inda suka ambaci "wulaƙancin" da aka yi musu a filin jirgin sama na Libya.

A wata sanarwa da CAF ta fitar ranar Litinin, ta ce "tana tattaunawa da hukumomin Nijeriya da na Libya bayan an sanar da ita cewa an yi watsi da tawagar ta 'yan wasan Nijeriya (Super Eagles) da masu horar da su, an kuma bar su cikin mawuyacin hali tsawon sa'o'i a wani filin jirgin sama, wanda hukumomin Libya suka umarce su su sauka."

CAF ta ƙara da cewa: "An miƙa batun ga Hukumar Ladabtarwa ta CAF domin bincike, kuma za a ɗauki matakan da suka dace kan duk waɗanda suka saɓa Matakan CAF da Dokokinta."

'Yan wasan na Nijeriya sun ce an yi watsi da su a filin jirgin sama na Libya tsawon fiye da awa 12 a ranar Litinin.

Sun sauka a nisan kilomita 200 daga masaukinsu

'Yan wasan na Super Eagles da ma'aikata sun tashi zuwa Libya ranar Lahadi da daddare, sai dai an karkatar da jirginsu zuwa filin jirgin sama na Al Abraq na Ƙasa-da-Ƙasa, maimakon na Benghazi inda da farko nan aka tsara za su sauka, wanda ya zarce nisan kilomita 200, kuma sai an yi tafiyar awa uku da rabi kafin a je otal ɗinsu.

Ɗaya daga jami'an Filin Jirgin Saman na Al Abraq na Ƙasa-da-Ƙasa ya shaida wa manema labarai cewa tawagar ta Nijeriya ta ƙi buga wasan ne a Libya don ƙaurace wa wasan neman shiga gasar AFCON da Libya a ranar Talata.

Jami'in ya ce 'yan wasan na Nijeriya sun yanke hukuncin koma wa gida ne maimakon buga wasan. Wasu daga 'yan wasan sun yi zargin cewa an bar su ba tare da abinci da ruwa ba.

Ita ma tawagar 'yan wasan Libya ta fuskanci irin wannan yanayi gabanin wasan neman shiga Gasar ta AFCON a Nigeria ranar 11 ga watan Oktoba, kamar yadda rahotannin kafofin watsa labaran Libya suka nuna.

'Ramuwar gayya'

Rahotannin sun ce "an sauke tawagar Nijeriya a filin jirgin Al Abraq "a matsayin ramuwar gayya."

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Libya (LFF) ta mayar da martani kan jinkirin da tawagar Nijeriya ta fuskanta, inda ta ce matsaloli ne da aka saba fuskanta na sauka da tashi da na aiki suka janyo shi.

"Muna musanta duk wani zargi na cewa da gangan aka tsara lamarin ko kuma akwai wata manufa kan abin da ya faru," a cewar LFF.

TRT Afrika