A matsayina na Babban hafsan sojojin na Nijeriya, amsa ta a ga masu kiraye-kiraye don juyin mulki mai sauƙi ce, ‘Mun gode, amma ba za mu yi abin da kuke so ba, in ji Laftanar Janar Taoreed Lagbaja./Hoto:Rundnar Sojojin Nijeriya

Babban Hafsan rundunar sojojin ƙasa ta Nijeriya Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya yi watsi da masu kiraye-kiraye ga sojoji su kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya a ƙasar.

Laftanar Janar Lagbaja ya bayar da tabbacin ne ranar Talata a jawabin da ya gabatar a taron manyan sojoji na shekara-shekara da ya jagoranta a birnin Uyo na Jihar Akwa Ibom da ke kudu maso kudancin ƙasar.

Babban Hafsan sojojin na Nijeriya na mayar da martani ne ga mutanen da suka gudanar da zanga-zanga ta kwana goma kan tsadar rayuwa wadda aka soma ranar 1 ga watan Agustan da ya gaba. Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun riƙa kiraye-kiraye ga sojojin Nijeriya su kifar da gwamnatin dimokurɗiyya.

Sai dai a jawabinsa a wurin taron, Laftanar Janar Lagbaja ya ce har yanzu sojojin Nijeriya suna ƙoƙarin maido da ƙimarsu da ta zube sakamakon juye-juyen mulkin da suka kwashe tsawon shekaru suna yi a ƙasar.

Don haka ne ya ce ba zai shige gaba don sake zubar da mutuncin sojoji ba ganin cewa an kwashe shekaru 25 ana gudanar da mulkin dimokuraɗiyya ba tare da juyin mulkin soji ba.

“Wani muhimmin batu da ya taso lokacin da aka gudanar da zanga-zanga shi ne kiraye-kiraye ga rundunar sojojin Nijeriya domin kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya.

“Duk da yake matasa ne suke waɗannan kiraye-kiraye waɗanda ba su taɓa fuskantar zafin mulkin soji ba da kuma fafutukar da gwarazan da suke cikin wannan zamani na dimokuraɗiyya suka yi wajen maido da ƙasar nan kan hanyar da take kai,"in ji shi.

Laftanar Janar Lagbaja ya ƙara da cewa, “A matsayina na Babban Hafsan sojojin ƙasa na Nijeriya, amsa ta a ga masu kiraye-kiraye don juyin mulki mai sauƙi ce, ‘Mun gode, amma ba za mu yi abin da kuke so ba! Rundunar sojojin Nieriya ba za ta bari a yi amfani da ita ba wajen kawo wasu marasa kishin dimokuraɗiyya kan mulki."

TRT Afrika