Ayyukan da ‘yan Nijeriya ke sa rai sababbin ‘yan Majalisar Dokoki su yi wa kasar

Ayyukan da ‘yan Nijeriya ke sa rai sababbin ‘yan Majalisar Dokoki su yi wa kasar

Akwai wasu ayyuka muhimmai da masana ke ganin su ya kamata mambobin sabuwar majalisar su mayar da hankali a kansu.
Karo na 10 kenan ta Majalisar Dokokin Nijeriya /Hoto: Nigerian Senate

Daga Halima Umar Saleh

‘Yan majalisar dokokin Nijeriya ta 10 na shan rantsuwar fara aiki a ranar Talatar nan 12 ga watan Yunin 2023.

Mutum 469 ne za su sha rantsuwar kama mulki da suka hada da ‘yan majalisar wakilai 360 da kuma ‘yan majalisar dattijai 109.

Wadannan wakilai na ‘yan Nijeriya sun fito ne daga jihohi 36 da kuma Abuja babban birnin kasar kuma karkashin jam’iyu daban-daban.

Kamar sauran shugabannin da aka rantsar a karshen watan Mayun da ya gabata -wato shugaban kasa da mataimakinsa da gwamnoni, su ma wadannan ‘yan majalisa akwai dumbin abubuwa da ke gabansu da ‘yan Nijeriya ke muradin ganin sun gudanar.

A hirarsa da TRT Afrika, Auwal Musa Rafsanjani, shugaban Cibiyar Inganta Aikin majalisun dokoki da Yaki da Cin Hanci a Nijeriya, CISLAC, ya ce babban fatan da ake da shi a kan wannan sabuwar majalisa da mambobinta shi ne yin dokokin da za su inganta rayuwar 'yan kasar sannan kada ta zama ‘yar-amshin-shata.

“Mun ga yadda majalisa ta tara ta ki mayar da hankali a kan yaki da cin hanci da rashawa, da kuma gaza sa ido kan yadda ake tafiyar da kudaden tallafin man fetur a kasar.

“Sannan mun ga yadda ita majalisa da taran dai ta ki bin diddigin gwamnatin da ta gabata kan tsarin karbo bashi daga kasashen waje inda ta dinga karya dokar kasa wajen karbo bashi. Ba ma fatan hakan ta sake faruwa a majalisa ta 10,” in ji masanin.

Malam Musa Rafsanjani ya ce ya kamata majalisa ta 10 ta dauki darasi kan wadannan abubuwa don gudun maimaita kura-kuran da aka yi a baya, “sannan ka da ta biye wa shugaban kasa kan muradunsa in dai ba a hurumin da ya dace ba.”

Koren Zaure shi ne na 'yan majalisar wakilai mai mambobi 360 /Hoto: Reps

Ga dai wasu ayyuka muhimmai da Rafsanjani ke ganin su ya kamata mambobin sabuwar majalisar su mayar da hankali a kansu:

  • Su yi fatali da duk tsarin da zai zama zalunci ga ‘yan Nijeriya
  • Su kawo gyara wajen tabbatar da aikin da majalisar take yi kamar ayyukan bayar da kwangila na Public Procurement da majalisa ta tara ta ki mayar da hankali a kai
  • Su rika tantance kasafin kudi dalla-dalla, “ba wai kawai a kai musu kasafi a gaya musu yadda ake so su aiwatar da shi ba
  • Su yi kokarin kawo gyararraki kan dokokin da ke bukatar gyara da kawo sababbin dokoki masu amfani
  • Su yi shugabanci ta wajen ba da misali da kansu.

Muhimman kudurori da ake sa ran Majalisa ta 10 ta yi

Kamar yadda aka sani, daga cikin manyan ayyukan majalisar dokoki har da gabatar da kudurorin da ka iya zama dokoki.

Shugaban majalisar dattijai kan zama mafi karfin mulki na uku a Nijeriya bayan shugaban kasa da mataimakinsa /Hoto: Nigerian Senate

Hakan ne ya sa Rafsanjani ya ce akwai muhimman kudurori da za a so sabuwar majalisar ta tabbatar da ganin an yi dokoki a kansu.

1. Dokar bayar da kariya ga masu son tona asiri kan cin hanci da rashawa da cin zarafin dan adam, wato Whistle Blowing Policy.

“Idan babu wannan dokar to ‘yan Nijeriya da dama ba za su iya sakin jiki su ba da bayanai ba don babu mai ba su kariya,” a cewar shugaban CISLAC.

2. Gyara dokokin tsaro da kariya na Nijeriya, wato Security Sector Reform.

Masanin harkokin majalisar ya ce gyara a kundin tsarin tafiyar da tsaro da ma hukumomin tsaron abu ne mai muhimmanci.

“Majalisa na bukatar duba rashin nasarar da ake samu don kawo gyara.”

3. Majalisa ta 10 na bukatar yin nazari a kan bangarori da dama na kundin tsarin mulkin Nijeriya

Misali yin nazari kan dokar da ta bai wa ‘yan kasa damar amfana da zama a kowane yanki da mutum ya samu a kansa a cikin kasar, musamman idan ana amfana da shi ta wajen samun haraji.

4. Majalisa ta 10 na bukatar sake yin nazari a kan dokar amfani da kasa ta Land Use Act, saboda irin matsaloli da badakalar da ke baibaye da ita,” in ji Rafsanjani.

5. Gyara kan dokar raba daidai wato Power Sharing Act. A cewar Auwal Rafsanjani dole ne majalisa ta 10 ta mayar da hankali wajen gyara a kan wannan batu, musamman kan yadda za a dinga rabon arzikin kasa da shugabanci.

“Majalisa na bukatar duba rashin nasarar da ake samu don kawo gyara,” in ji Auwal Musa Rafsanjani shugaban Cibiyar CISLAC

“Hakan zai kawo karshen rigingimu da rashin kwanciyar hankali irin siyasa da tattalin arziki da yaki da talauci. Idan ba haka ba kuwa to za a bar jihohi a baya sosai musamman ma jihohin arewa,” a cewar masanin.

6. Samar da dokar gyara a fannin shari’ar Nijeriya ma na daga cikin muhimmai da za a sa ran ganin majalisa ta 10 ta dauki mataki a kai. “Dole a dawo da martabar shari’a,” Rafsanjani ya kara da cewa.

Yadda tsarin majalisar dokokin Nijeriya ke aiki

Ginin majalisar dokokin Nijeriya yana yankin da ake kira “Three Arms Zone” a babban birnin tarayya Abuja, wanda ya ƙunshi fadar shugaban ƙasa da majalisar dokoki da kuma Kotun Koli.

Katafaren ginin na kunshe da manyan zauruka biyu; wato Jan Zaure, “Red Chamber”, inda can ne ‘yan majalisar dattijai ke zamansu da gudanar da muhawara da kuma gabatar da kudure-kudurensu.

Sannan kowane dan majalisa yana da ofishi daban a cikin ginin da kowa ke gudanar da ayyukansu.

Akwai kuma zaurukan da kwamitoci ke haduwa don ganawa kan abubuwan da suka bijiro masu alaka da ayyukansu.

Sanatoci 109 ne mambobinta, wadanda suka fito daga jihohin Nijeriya 36, wato uku daga kowace jiha, da ke wakiltar yankunan arewa da kudu da tsakiyar jihar, sai kuma daya mai wakiltar birnin tarayya Abuja.

Shugabancin majalisar ya hada da:

  • Shugaban Majalisar Dattaijai
  • Mataimakin Shugaban Majalisar Dattaijai
  • Shugaban Masu Rinjaye
  • Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye
  • Shugaban Marasa Rinjaye
  • Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye
  • Bulaliyar Majalisa
  • Mataimakin Bulaliyar Majalisa
  • Bulaliyar Majalisa na Marasa Rinjaye
  • Mataimakin Bulaliyar Majalisa na Marasa Rinjaye.

Mambobin majalisun biyu su 469 ne da suka hada da ‘yan majalisar wakilai 360 da kuma ‘yan majalisar dattijai 109 /Hoto: Senate President

A can Koren Zaure kuwa (Green Chamber), akwai ‘yan majalisar wakilai 360 da suka fito daga kowace jiha ta fadin kasar, kuma yawan su ya danganta ne da girman jihar.

Shugabanci a majalisar wakilai na farawa ne daga kan:

  • Shugaban Majalisa
  • Mataimakin Shugaban Majalisa
  • Shugaban Masu Rinjaye
  • Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye
  • Shugaban Marasa Rinjaye
  • Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye
  • Bulaliyar Majalisa
  • Mataimakin Bulaliyar Majalisa
  • Bulaliyar Majalisa na Marasa Rinjaye
  • Mataimakin Bulaliyar Majalisa na Marasa Rinjaye.

Babban Aikin Majalisa

  • Yin dokokin da za su kawo ci gaban kasa da zaman lafiya da kwanciyar hankali
  • Wakilci don tabbatar da ana damawa da kowane bangare na kasar
  • Sa ido kan hukumomi da ma'aikatu da tsare-tsaren gwamnati
  • Yin bayani dalla-dalla na irin wakilcin da suke yi wa al’ummominsu da jin koke-koken mazabunsu da neman shawarwari kan inganta ayyukansu
  • Bai wa shugaban kasa izinin nada ministoci ko ciyo bashi.

TRT Afrika