Ana gudanar da taro a Mauritania ranar Laraba game da yadda za a warware rikicin Sudan wanda wakilai daga Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙasashen da ke shiga tsakani da kuma ƙungiyoyi za su halarta.
Gidan rediyon gwamnatin Mauritania ya ruwaito cewa Shugaba Mohamed Ould Ghazouani ya tarbi Ramtane Lamamra, Wakili na Musamman kan Sudan na Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres Sudan, Ramtane Lamamra,a Fadar Shugaban Ƙasa da ke birnin Nouakchott.
Ganawar tasu ta mayar da hankali kan yadda za a warware rikicin ƙasar Sudan, musamman batun kai kayan agajin jinƙai.
Ministan Harkokin Wajen Mauritania Mohamed Salem Ould Merzoug ya sanar cewa ƙasarsa za ta karɓi baƙuncin taron da zai haɗa masu ruwa da tsaki kan warware rikicin Sudan.
Tun a watan Afrilun 2023 ne rikici ya ɓarke tsakanin sojojin Sudan da rundunar kai ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces (RSF) kan dalilai na siyasa.
Rikicin ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 20,000, sannan ya raba miliyoyi da gidajensu, kana fiye da mutum miliyan 25 na matuƙar buƙatar agajin gaggawa, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.