Masana sun ce Nijeriya na bukatar karin hanyoyin samun kudi bayan danyen mai/Photos:Reuters

Masana tattalin arziki a Nijeriya sun yi gargadi cewa kasar ka iya fadawa cikin matsalar tattalin arziki irin wanda Sirilanka ta fada, idan har ta cigaba da biyan kudin ruwan basussukan da ake bin ta da kudaden shigar da take samu.

Gargadin masanan na zuwa ne a matsayin martani kan wani sabon rahoto da Bankin Duniya ya fitar da ke cewa kudin ruwan da Nijeriya ke biya kan basussukan da ake bin ta ya kai kashi 96.3 cikin 100 na kudaden shigar da take samu.

A hirarsa da TRT Afrika Dakta Abubakar Abdullahi, malami a fannin koyar da Tsimi da Tanadi a Jami’ar Jihar Kaduna, ya ce rahoton, wanda ke nazari kan talauci a kasashen duniya, na nuna "wata babbar matsalar tattalin arziki da Nijeriya ke fuskanta.”

Me rahoton ya kunsa?

Rahoton Bankin na watan Afrilu ya ce duk da cewa bankunan kasar na nan garau, matsalolin kasafin kudi da kuma matsalolin kasashen waje ka iya janyo tsaiko ga bangaren tattalin arzikin kasar.

“A shekarar 2022, kudin tallafin mai ya karu daga kashi 0.7 cikin 100 zuwa kashi 2.3 cikin 100 na ma’aunin tattalin arziki (GDP),” a cewar rahoton.

Ya ce karancin kudin shiga da ba na mai ba da kuma yawan kudin ruwa sun kara matsalar kasafin kudin kasar.

A shekarar 2022, kudin da kasar ta kashe ya fi kudin da ta samu da kashi 5.0 cikin 100 na ma’aunin tattalin arzikin kasar.

Wani masani ya ce ya kamata a yi wa bangaren shari’a garambawul ta yadda kotu za ta iya yanke hukunci cikin kankanin lokaci /Hoto: Presidency

“Wannan ya sa bashin da ake bin kasar ya haura kashi 38 cikin 100 na ma’aunin tattalin arziki, kuma ya kara kudin ruwan da kasar ke biya daga kashi 83.2 cikin 100 zuwa kashi 96.3 na kudin da kasar ta samu a shekarar 2022,” a cewar rahoton.

Me hakan ke nufi ga kasar?

A daidai lokacin da hasashe ke nuna cewa yawan mutane a Nijeriya zai rinka karuwa da kashi 2.4 cikin 100, wani hasashen kuma ya nuna cewar tattalin arzikin kasar zai habaka da kashi 2.9 cikin 100 nan da shekarar 2025 , in ji rahoton.

Ya ce idan karuwar yawan mutanen Nijeriya ya ci gaba har ya zarce yawan mutanen da ake fitar wa daga talauci, sannan farashin kayayyaki suka cigaba da hawa, mutum miliyan 13 za su sake shiga cikin talauci daga yanzu zuwa shekarar 2025 a kasar.

Rahoton ya ce idan ba a cire tallafin kudin mai a watan Yunin shekarar 2023 ba, matslar kasafin kudin kasar za ta kada ta’azzara.

Dakta Abubakar ya kara da cewar aron kudi don biyan kudin ruwa ko don samun na kashewa wani yanayi ne da ba zai dore ba.

A cikin watan Yuni ne dai kasar za ta cire tallafin mai/ Hoto: Reuters

Mafita

Dr Abubakar ya ce "akwai bukatar gaggawa ta sake nazari kan abubuwan da muka bai wa muhimmanci, mu sake tsare-tsaren tattalin arzikinmu mu kuma bude sababbin hanyoyin samun kudin shiga.”

Baya ga haka Nijeriya na da bukatar karfafa ma’aikatun gwamnati don iya yaki da cin hanci da rashawa ta yadda za a iya tuhumar wadanda suke rike da mukaman gwamnati idan suka aikata ba daidai ba, a cewarsa.

Ya kara da cewa ya kamata a yi wa bangaren shari’a garambawul ta yadda kotu za ta iya yanke hukunci cikin kankanin lokaci.

Dr Abubakar na ganin Nijeriya na bukatar daina dogaro kan danyen mai a matsayin hanyar samun kudaden shiga daya tilo, ta kuma mayar da hankali wajen samun kudi ta wasu hanyoyin.

Masana sun ce Nijeriya na bukatar sake yi wa tattalin arzikinta garambawul/ Hotos: Reuters

Har ila yau, malamin ya ce ya kamata a toshe hanyoyin da kudaden gwamnati ke yoyo domin kara wa gwamnati kudin shiga.

Ya ce idan aka yi hakan, tattalin arzikin Nijeriya zai fice daga wannan mawuyacin halin.

TRT Afrika da abokan hulda