Farashin abinci ya ƙaru daga kashi 40.53 zuwa kashi 40.66 a watan na Mayu, a cewar hukumar NBS./Hoto: Reuters

A ranar Lahadi ne ake gudanar da bukukuwan Babbar Sallah a Nijeriya kamar sauran sassan duniya, kwana guda bayan alhazai sun sauko daga Arafat a Saudiyya.

Miliyoyin 'yan Nijeriya na gudanar da bukukuwan ne a yayin da ƙasar take fama da matsin tattalin arziki mai munin gaske sakamakon hauhawar farashi bayan janye tallafin man fetur da aiwatar da wasu sauye-sauye kan tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi.

Alƙaluman da hukumar ƙididdiga ta Nijeriya (NBS) ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa hauhawar farashi ta ƙaru da kashi 33.95 a Mayu, wanda shi ne adadi mafi girma a cikin shekaru 28 da suka gabata.

Farashin abinci ya ƙaru daga kashi 40.53 zuwa kashi 40.66 a watan na Mayu, a cewar hukumar.

'Mummunan yanayi'

Ibrahim Dan'azumi, wani ma'aikacin gwamnati a ƙaramar hukumar Jibia da ke Jihar Katsina, ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa mummunan yanayin da suke ciki ba zai taɓa misaltuwa ba saboda tashin farashin kayayyaki.

"A baya mukan sayi kayan abincin da zai kai kwana goma zuwa sha biyu, amma yanzu albashin mutum ba zai ishe shi ko da kwana biyar ba saboda hauhawar farashin kayayyaki. Mudun shinkafa ya kai N3600 zuwa 4,000 a ƙasar da har yanzu mafi ƙarancin albashi bai wuce N3,000 ba," in ji shi.

Shi ma Garba Rabiu Kura, wani magidanci da ke jihar Kano, ya ce yanzu ana rayuwa ne hannu-baka-hannu-ƙwarya domin kuwa komai ya taɓarɓare.

A cewarsa, "Duk abin da ka sani ya tashi a ƙasar nan. Daga kayan abinci zuwa kayan sawa da komai. Yanzu ba ta kayan sallah ake ba, ana maganar yadda za a rayu ne. Shi ya sa muka bai wa iyali haƙuri cewa ba za su samu kayan sallah ba. Ita layya tun da ba wajibi ba ne, ko tunaninta ba mu yi ba domin kuɗin rago ɗaya yakan kai N100,00. Ka ga kuwa albashin fiye da mutum uku ke nan."

Masana sun ce an dade ana hasashen hauhawar farashi za ta ci gaba a Nijeriya /Hoto: Getty Images

Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na Nijeriya ta tsunduma yajin aiki a faɗin ƙasara farkon watan nan don matsa wa gwamnati ƙara albashi da neman janye ƙarin da aka yi na kuɗin lantarki a faɗin ƙasar.

Sai dai daga bisani ta dakatar da yajin aikin sannan suka ci gaba da tattaunawa kan lamarin.

Kawo yanzu dai gwamnatin Nijeriya ta yi tayin biyan ma'aikatan ƙasar N62,000 duk wata a matsayin mafi ƙarancin albashi ko da yake 'yan ƙwadagon sun kafe cewa dle ta riƙa bai wa ma'aikata N250,000, maimakon N494,000 da a baya suka nemi gwamnati ta riƙa biya.

TRT Afrika