Yajin aikin masu gidajen man ya shafi jihohin Adamawa da Taraba na Nijeriya. / Photo: Getty Images

Kusan gidajen mai 2,000 aka rufe a yankin Arewa maso gabashin Nijeriya, don nuna adawa da ayyukan hana fasa-ƙwauri da hukumomi suke yi domin daƙile masu safarar man zuwa wajen ƙasar.

Shugaban ƙungiyar 'yan kasuwar man da ke yankin, Dahiru Buba, shi ne ya sanar da haka ranar Litinin, kuma matakin ya sa masu motoci komawa sayen mai daga wajen 'yan bumburutu.

Dahiru Buba, wanda shi ne shugaban 'yan kasuwar man fetur masu zaman-kansu ta IPMAN, shiyyar jihohin Adamawa da Taraba, ya ce gidajen mai sun dakatar da aiki bayan da hukumar hana fasa-ƙwauri ta Nijeriya ta ƙwace tankokin mai, kuma ta rufe wasu gidajen mai saboda zargin suna safararsa zuwa ƙasar Kamaru da ke maƙwabtaka.

Cikin tsawon shekaru, masu sayar da mai a kasuwannin bayan fage da ke Kamaru, da Benin da Togo, suna dogaro ne kan mai, mai sauƙin farashi da ake safara ta ɓarauniyar hanya daga Nijeriya.

Lokacin da Nijeriya ta soke tallafin mai a bara, kasuwanci a kasuwannin bayan fage ya tsaya. Amma farashin man ya sake komawa mai sauƙi a Nijeriya bayan da gwamnati ta ƙayyade farashin tun a Yunin 2023, duk kuwa da darajar kuɗin ƙasar ta ragu sosai.

Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta ƙaddamar da yaƙi kan hana fasa-ƙwaurin mai, wanda ta kira da yaƙin "Operation Whirlwind", inda ta fara ƙwace wasu tankokin mai mallakin mambobin IPMAN, sannan ta sake su bayan ƙungiyar ta koka.

A cewar Buba, an kuma ƙwace wasu ƙarin motocin dakon man, sannan aka rufe wasu gidajen mai, wanda hakan ne ya janyo masu gidajen man suka rurrufe da yawan gidajen mansu don nuna rashin amincewa.

"Mun ƙara rubuta wa (Hukumar Kwastam ta Nijeriya) wasiƙa amma ba mu samu martani ba, shi ya sa muka yanke shawarar shiga yajin aiki," in ji Buba, wanda kuma ya ƙara da cewa gidajen mai 1,800 sun daina aiki.

"Wannan ne kasuwancinmu, kuma ba za mu rufe baki ba yayin da ake cin zarafin mambobinmu."

Kakakin hukumar Kwastam shiyyar jihohin Adamawa da Taraba, Mangsi Lazarus, ya ce an ƙwace motocin dakon man ne saboda ana amfani da su wajen fasa-ƙwaurin mai.

A babban birnin jihar Adamawa, Yola, 'yan bumburutu sun yi amfani da wannan dama ta ƙarancin mai, inda suke sayar da litar mai kan Naira 1,400, idan aka kwatanta da farashin Naira 650 zuwa 750 da aka saba sayarwa.

Reuters