Rundunar 'yan sandan Nijeriya reshen Jihar Ribas ta mamaye sakateriyar dukkan ƙananan hukumomi 23 na Jihar da wasu muhimman gine-gine sakamakon rikicin shugabanci.
Rikicin ya kunno kai ne bayan a ranar Talata gwamnan jihar Siminalayi Fubara ya umarci shugabannin ƙananan hukumomi na riƙo da ya naɗa su karɓi ragamar shugabanci daga shugabannin da wa'adinsu ya ƙare ranar Litinin.
Sai dai bayanai sun ce 21 daga cikin shugabanni 23 da wa'adinsu ya ƙare sun ƙi sauka daga kan mulki, lamarin da ya haddasa zaman ɗardar.
Hakan ne ya sa rundunar 'yan sandan jihar ta Ribas ta aike da jami'anta don su sanya ido kan lamarin da ke faruwa. Sai dai wasu bayanai sun ce hatsaniyar da aka yi a wata ƙaramar hukuma ta yi sanadin mutuwar jami'an tsaro biyu.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Ribas Grace Iringe-Koko ta tabbatar wa Channels Television mutuwar jami'an tsaro biyu.
Ta ƙara da cewa ɗan sanda ɗaya da wani ɗan bijilanti ne suka mutu, ko da yake ba ta bayyana abin da ya kai ga mutuwar tasu ba. Sai dai bayanai sun ce sun mutu ne a garin Eberi-Omuma, hedkwatar ƙaramar hukumar Omuma kuma mutuwar tasu na da alaƙa da mamayar da 'yan sanda suka yi wa sakateriyar garin.
Iringe-Koko ta ce an soma gudanar da bincike kan lamarin sannan an tura ƙarin 'yan sandan kwantar da tarzoma yankin.
Gwamna Siminalayi Fubara ya gana da shugabannin jami'an tsaro da ke jihar kuma daga bisani ya shaida wa manema labarai cewa sun tattauna ne kan mamayar da 'yan sanda suka yi wa sakateriyar ƙananan hukumomin da kuma yadda za a warware matasalar.
Jihar Ribas ta faɗa rikicin siyasa tun bayan da aka samu rashin jituwa tsakanin Gwamna Fubara da uban gidansa na siyasa kuma tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike, wanda yanzu shi ne Ministan Babbar Birnin Tarayya, Abuja.