Wani ƙudirin doka da ke neman a dinga bai wa masu takaba hutun watanni biyar ya yi nasarar tsallake karatu na biyu a zauren majalisar wakilai ta Nijeriya.
Ɗan majalisa Saidu Abdullahi ne ya samar da ƙudurin don a dinga bai wa mata da maza da abokan zamansu suka rasu isasshen lokacin yin alhini da kuma samun damar shirya wa ƙalubalen da ke gaba, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.
Honorabul Saidu ya ce akwai buƙatar yin la’akari da ƙudurin saboda dalilai na addini da al’ada.
Ya ce an tsara wannan ƙudirin ne domin sanya Nijeriya a jerin kasashen da ke kan gaba a fannin walwalar ma’aikata kasancewar akwai dokar a kasashe da dama.
A cewarsa, binciken da aka gudanar ya nuna cewa a Nijeriya, hukumomi da ma’aikatun gwamnati kan ba da hutun kwanaki 14 ne kawai ga ma’aikatan da abokan zamansu.
Sai dai ya ce kwanaki 14 sunyi kadan idan aka yi duba da yanayin al’adu da addini a Nijeriya.
Shugaban majalisar, Tajudeen Abbas ya miƙa ƙudurin ga Kwamitin Sauye-Sauyen Bangarorin da suka shafi Jama’a don ƙara nazari.
Wasu addinan sun tanadi tsawon lokacin da ya kamata masu takaba su yi kafin komawa harkokinsu na yau da kullum. Alal misali a Musulunci, ana so mace ta yi takabar rasuwar mijinta har tsawon wata huɗu da kwana 10.