Afunanya ya ce ana tsare 'yan ƙasar Poland din ne a lokacin da hukumar DSS ke ƙoƙarin tabbatar da tsaro. Hoto  AA

Nijeriya ta kama wasu 'yan kasar Poland bakwai da suka ɗaga tutocin kasar Rasha yayin zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a makon nan a jihar Kano da ke arewacin kasar, in ji kakakin hukumar tsaro ta farin kaya DSS, Peter Afunanya a ranar Laraba.

Dubban ‘yan Nijeriya ne suka fara zanga-zangar tun ranar 1 ga watan Agusta domin nuna rashin amincewarsu da sauye-sauyen tattalin arziki da Shugaba Bola Tinubu ya yi wanda ya kawo karshen tallafin man fetur da wutar lantarki da rage darajar kudin kasar da hauhawar farashin kayayyaki a tsawon shekaru uku.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce zanga-zangar da ta rikide zuwa rikici ta yi sanadin mutuwar mutane akalla 6 a jihohin arewacin kasar, kawo yanzu an kashe mutane 22 a yayin zanga-zangar, in ji kungiyar kare hakkin bil adama.

A wannan makon wasu masu zanga-zangar sun daga tutocin kasar Rasha yayin zanga-zangar da aka yi a jihohin arewacin kasar, lamarin da ke nuna damuwa kan karuwar ayyukan da Rasha ke yi a yammacin Afirka. Jami’an tsaro sun tsare wasu teloli da suka ce sun ɗinka tutocin.

'Ba 'yan ƙasar Poland ake fakowa ba'

Afunanya ya ce ana tsare 'yan ƙasar Poland din ne a lokacin da hukumar DSS ke ƙoƙarin tabbatar da tsaro,

Bai yi ƙarin bayani a kan ko su waye su ba, amma ya ce ba a ƙadamar da samamen don a far wa 'yan ƙasar Poland ɗin ba.

Wani jami'in diflomasiyyar Poland a Nijeriya Stanislaw Gulinski, ya tabbatar da batun kamen a wata ganawa da ya yi da jami'an diflomasiyyar Ma'aikatar Harkokin Wajen Nijeriya Stanislaw Gulinski a Abuja.

“An kama su ne kwanaki biyu da suka gabata a Kano, kuma a karshe na ji suna cikin jirgi zuwa Abuja daga Kano,” in ji shi.

'Laifin cin amanar ƙasa'

Gulinski ya ƙi cewa komai a lokacin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tuntuɓe shi don yin tsokaci.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Poland ta rubuta a dandalin sada zumunta na X cewa: "An sanar da ofishin jakadanci da ke Abuja game da kama wasu dalibai 'yan Poland da wani malami a Kano da ke, arewacin Nijeriya."

"Ma'aikatar kula da harkokin waje tana gudanar da bincike kan hakikanin lamarin tare da hukumomin kasar domin tallafa wa 'yan kasarmu. Ma'aikatar harkokin waje na ci gaba da tuntubar iyalan wadanda aka tsare."

Babban hafsan tsaron Niojeriya, Janar Christopher Musa, ya kira sanya tutar kasashen waje yayin zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a matsayin wani laifi na cin amanar kasa bayan ya tattauna kan tsaro da Shugaba Bola Tinubu a ranar Litinin.

Rasha ta musanta hannu a lamarin

A jihohin Borno da Kaduna da Kano da Katsina, an ga masu zanga-zangar suna daga tutocin kasar Rasha, inda wasu ke kira da a karbe ikon kasar.

Ofishin jakadancin Rasha da ke Nijeriya ya musanta hannu a lamarin.

Reuters