Gwamnatin Jihar Kano ta ɗaura auren mata 1,800 da angwayensu 1,800 da ta dauki watanni tana shiryawa, a yau Juma’a 13 ga watan Oktoba.
Tun bayan hawansa mulki ne, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar ya sanar da cewa zai yi wa matan da ba su da galihu auren gata, ta hanyar samar musu da dukkan kayayyakin da mace ke bukata a gidan aure da kuma yi musu walicci.
An ɗaura aurarrakin ne a wasu masallatan Juma'a a dukkan ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar.
A babban Masallacin Juma’a na gidan Sarkin Kano kawai an daura auren kusan mutum 300 wanda shi ne Gwamna Abba Kabir Yusuf da shugaban Hisbah Sheikh Aminu Daurawa, wanda shi ne jagoran hidimar suka halarta.
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne waliyyin angwaye yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zama waliyyin amare a kan sadaki Naira 50,000 ga kowace amarya.
Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi na daga cikin wadanda suka harlaci daurin auren.
Tun a wata hira da ya yi da TRT Afrika kwana biyu kafin daurin auren, Kwamandan Hisbah Sheikh Daurawa ya ce tuni an kammala da matakai biyar cikin bakwai na auren.
“Tsari ya kusa zuwa ƙarshe na auren zawarawa da ’yan mata. An ɗauki matakai bakwai kuma an cimma biyar zuwa yanzu,” in ji Malam Daurawa a wata hira da yi da TRT Afrika, ana saura kwana biyu a ɗaura auren.
Ga dai matakan da babban malamin ya bayyana na yadda shirye-shiryen auren ya kasance tun daga farko:
Matakin farko shi ne gabatar da shirin da gwamnan Kano Abba K Yusuf ya yi na bayyana aniyar aurar da ‘ya’yan talakawa da iyayensu ba su halin aurar da su, inda aka nemi masu bukatar shiga cikin tsarin da su je su karbi fom a hukumar Hisbah.
Mataki na biyu shi ne na tantancewa aka zaɓi waɗanda za su shiga tsarin.
Mataki na uku shi ne kai su asibiti don tantance lafiyarsu, inda aka samu masu ɗauke da cutar HIV da masu Hepatitis da waɗanda nau’in jininsu bai dace da juna ba, “sai kuma waɗanda aka same su da ciki da ba su wuce biyu ko uku ba,” in ji Sheikh Daurawa.
Ya ce likitoci sun ba da shawarar cewa akwai waɗanda za su sha magani daga baya a yi auren. Akwai waɗanda kwata-kwata kuma ma auren ba zai yiwu ba.
Mataki na huɗu shi ne na yi wa ma’auratan bita a kan zaman aure da aka yi a gidan gwamnatin Jihar Kano a ranar Laraba 11 ga watan Oktoba.
An gayyaci wasu farfesoshi biyu masana halayyar ɗan’adam daga Jami’ar Bayero sai kuma shi Shugaban Hisban Sheikh Daurawa da mataimakiyarsa a ɓangaren mata Dr Khadijah Sagir Sulaiman.
Mataki na biyar shi ne “ɗaura auren mutum 1,800 ɗin da za a yi a faɗin masallatan Jihar Kano, kowace ƙaramar hukuma za ta aurar da nata amaren ranar Juma’a 13 ga watan Oktoban 2023,” a cewar Kwamandan Hisbah.
Sannan a ranar Asabar 14 ga watan Oktoba za a gudanar da walima a gidan gwamnati, inda Gwamna Abba Gida-Gida ya gayyato baƙi har daga ƙasashen waje, kamar yadda Sheikh Daurawa ya sanar da TRT Afrika.
Mataki na shida a cewar malamin shi ne za a rabawa matan kayayyakin da aka yi alkawari wato gado da katifa da matasan kai da zanin gado da ledar tsakar daki da buhun shinkafa ɗaya da katan ɗin taliya ɗaya da katan na indomi ɗaya da jarkar mai ɗaya.
Sai sadakin naira 50,000 da kuma jarin naira 20,000 da za a bai wa kowaccensu don kama sana’a.
Mataki na bakwai shi ne wanda hukumar Hisbah za ta saka ido don tabbatar da tarewarsu. “Dama tuni an buƙaci kowanne ango ya nuna wajen da zai ajiye amaryarsa, ko a gidansa na kansa ko na haya ko ma na aro ne, dole sai da duk angwayen suka nuna mana mazaunan amaren kafin a kawo wannan gaɓa ta ɗaura aure,” Kwamandan Hisbah ya ce.
Shugaban hukumar Hisban ya ce ko bayan auren akwai kwamitin da zai dinga bibiyar yadda zamantakewarsu take kasancewa, saboda ganin ana bin sharuɗɗan auren sau da ƙafa.
“Sharuɗɗan su ne babu saki ba yaji ba duka ba kora ba cin mutunci, idan an samu matsala a zo hisbah ita ce za ta warware komai,” ya faɗa.
Yabo da suka
Tun daga lokacin da aka fara batun wannan aure ne dai mutane da masu sharhi suka fara bayyana ra’ayoyi daban-daban kan lamarin.
Tsari ya kusa zuwa ƙarshe na auren zawarawa da ’yan mata. An ɗauki matakai bakwai kuma an cimma biyar zuwa yanzu.
Wasu na ganin ɓata kuɗin gwamnati ne kawai zai sa a ce za a aurar da mutum 1,800, maimakon a yi amfani da kuɗaɗen wajen magance wasu matsalolin da suke ci wa al’umma tuwo a ƙwarya.
Amma wasu na ganin daga cikin manyan matsalolin al’umma irin ta arewacin Nijeriya akwai yawan mace-macen aure da kuma mutane da dama da ke son yin auren amma ko kuɗin katifa ba su da shi.
Malam Aminu Daurawa ya ce tun da fari babban maƙasudin auren shi ne taimakawa mata musamman waɗanda iyayensu ba su da halin aurar da su, kuma babban sharaɗin auren shi ne ba a bai wa namijin da ba shi da sana’ar dogaro da kansa wacce kuma zai iya riƙe mace da ita.
“Sannan shi kansa jarin da ake bai wa amaren ba sakaka aka ba su ba, sai da aka koya musu yadda za su yi sana’a da shi.
“Don haka wannan tsari taimakawa tattalin arzikin mutane ne gwamnati ke yi ba ɓata kuɗin gwamnati ba."
Ba wannan ne karo na farko da ake irin wannan auren gata ba a Jihar Kano, an yi irin sa a can baya lokacin mulkin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Daurawa wanda shi ne dai shugaban Hisbah na lokacin.
Ganin yadda ake yawan samun mace-macen aure a arewacin Nijeriya ya sa TRT Afrika ta tambayi Malam Daurawa ko wacce irin nasara aka samu a aurarrakin wancan lokacin.
“Daga cikin alfanun da aka cimma har da cewa babu auren da ya taɓa mutuwa sai da sanin hukumar Hisbah, bisa dalili mai ƙarfi.
“An saka ido sosai, duk abin da ya taso wajen Hisbah ake zuwa. Makasudin hakan shi ne rage yawan mutuwar aure da muke fama da shi a cikin al’ummar nan.”
Kwamandan Hisban ya tabbatar da cewa ko a wannan karon ba za su sa ido ma’auratan su yi ta zama sakaka ba, dole hukumar za ta dinga bibiyar abubuwan da ke faruwa a gidajen auren.