Ronaldo ne ɗan wasa ɗaya tilo da ya ci bugun fenariti ɗinsa cikin duka bugun da ƴan wasan Al-Nassr suka buga./Hoto: Getty

Ƙungiyar Al-Ain ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta fitar da ƙungiyar Al Nassr wacce Cristiano Ronaldo ke yi wa wasa daga Gasar ƙungiyoyin nahiyar Asiya wato Asian Champions Leaguea a bugun fenariti da ci 3-1.

Al-Nassr ce ta fara yin rashin nasara a wasan farko da ƙungiyoyin biyu suka buga da ci 1-0, sai dai Al-Nassr ta sha kashi a gida a wasan da suka a jiya Litinin, inda aka tashi wasan 4-3, kafin daga bisani bugun fenariti ya raba-gardama a tsakaninsu.

Ronaldo ya ɓarar da wata babbar dama da ya samu yayin wasan, ko da yake ya yi nasarar cin bugun fenareti a minti na 118, abin da ya sa jimullar sakamakon wasannin biyu ya koma 4-4.

Ronaldo ne ɗan wasa ɗaya tilo da ya ci bugun fenariti ɗinsa cikin duka bugun da ƴan wasan Al-Nassr suka buga.

Sai dai a minti na 72 tsohon ɗan wasan Manchester United Alex Telles ya ci ƙwallo da ta tilasta aka tafi ƙarin lokaci bayan cikar minti 90, sannan an kori ɗan wasan Al Nassr Ayman Yahya bayan ya samu jan kati.

Yanzu ƙungiyar Al-Ain za ta san ƙungiyar da za ta fafata da ita a mataki na gaba na gasar a kwanakin da ke tafe.

TRT Afrika