A yayin da ‘yan Nijeriya ke cikin fargaba game da wasu rahotanni da ke cewa akwai yiwuwar a kara farashin man fetur, shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sanarwa cewa babu wani shiri na kara farashin fetur din.
Sai dai wannan tabbaci da shugaban kasar ya bayar ya sanya shakku a zukatan ‘yan Nijeriya ganin cewa tuni ya cire tallafin man sannan gwamnati ta bayyana cewa yanzu kasuwa ce za ta yi halinta kan farashin fetur - wato dai babu wani tsayayyen farashi.
‘Yan kasar sun yi ta kuka kan matsin da suke ciki sakamakon hauhawar farashin man fetur bayan Shugaba Tinubu ya janye tallafinsa a watan Mayun da ya gabata, inda litar mai ta kai har 620, sabanin farashin kasa da naira 200 a baya da gwamnati ta kayyade a hukumance.
Yaduwar wancan labari na fargabar kara farashin fetur ke da wuya sai fadar shugaban kasar ta fitar da sanarwar cewa sam babu wannan shirin a tsarinta.
Mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale, ya ce “Yau [Talata] da safe na gana da Shugaba Tinubu. Mun tattauna kan abubuwan da ke faruwa a kasa game da man fetur.
“Shugaban kasa yana jaddada matsayar kamfanin mai na ƙasa NNPCL cewa ba za a ƙara farashin man fetur ba yanzu. Muna ƙara jaddada hakan.''
To amma akwai tambayoyi birjik kan manufar wannan magana ta Shugaba Tinubu da ke cunkushe a zukatan ‘yan Nijeriya.
Bari mu duba su tare da fayyace abin da suke nufi daga mahangar masu sharhi.
1. Me kalaman shugaban Nijeriya ke nufi?
Kwararru a kan fannin man fetur a Nijeriya irin su Dr Ahmed Adamu na Jami'ar Umaru Musa Yar'adua da ke Katsina na ganin wannan batu na Shugaba Tinubu na nufin kwan-gaba-kwan-baya ne a batun janye tallafin fetur da gwamnatin ta yi.
“Kamata ya yi idan gwamnati ta zo da wani tsari na tattalin arziki ta tsaya tsayin daka a kansa, amma an cire tallafi mutane suka gama shan wahala, tattalin arziki ya tsuke kuma sai yanzu a ce za a dawo da shi?
Hakan na nufin wahalar da aka sha a baya ta tashi a banza kenan,” masanin ya koka. “Sannan to nan gaba za a sake cire shi ne? Idan kuma an sake cire shi din wane sauyi hakan zai kawo.”
A ganin masanin dama tun farko gwamnati ta yi gaggawa wajen cire tallafin man fetur.
Labari mai alaka: Ina jin radadin da kuke ji kan cire tallafin fetur – Shugaba Tinubu
Sai dai a nasu bangaren, kungiyar dillalan man fetur na Nijeriya na ganin wannan batu na Shugaba Tinubu abin a yi maraba da shi ne.
“Da farko mun zaci idan aka cire tallafin fetur wanda muma mun ba da goyon baya za a samu wadatuwar dala, tun da a baya wasu na zargin mu ne silar zirarewar wadannan kudade,” in ji Alhaji Bashir Danmalam, shugaban kungiyar dillalan fetur ta IPMAN.
“Shi ya sa muka ce to a cire tallafin a gani, idan mu ne za a gani, idan ma ba mu ba ne duk za a gani. Kuma mun gode Allah a yanzu da aka cire mutane sun yi alkalanci da kansu," Danmalam ya kara fada.
2. Ta ina maganar kara farashin man ta fara fitowa?
A bakin kakakin kungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya Cif Chinedu Ukadike aka fara jin batun karin farashin fetur din, inda ya ce ‘yan kasar su tsammaci tashin farashin mai saboda rashin daidaiton darajar naira a kasuwar musayar kudade.
Wannan lamari ya jefa miliyoyin al’ummar kasar cikin damuwa, har sai da kungiyoyin kwadago ma suka yi barazanar shiga zanga-zanga.
A hirarsa da TRT Afrika shugaban IPMAN wanda kuma shi ne shugaban kungiyar dillalan fetur da iskar gas na arewacin Nijeriya, Bashir Danmalam, ya ce ganin halin da al’umma ta shiga tun bayan hawan farashin ne da kuma yadda kasuwar ke musu ne ya sa suka yi magana.
“Mu muke tare da ala’umma muna ganin halin da suke ciki, mutane ba sa iya shan man ma, zirga-zirga ta tsaya, abubuwa sun yi zafi da yawa.
“Hatta masu gidajen man sai sun hadu kamar mutum biyu zuwa uku sannan suke iya sayen mota daya, shi ya sa muma muka fara kira cewa idan har ba a yi wani abu ba to fa farashin mai zai tafi inda ba a tunani."
Ya ce wannan dalili ne ya sa suka yi kira ga gwamnati da ta rage wa ‘yan kasa radadin farashin ko da na kashi 20 ne ko 30.
“Kuma Alhamdulillah shugaban kasa ya amsa ya ji wadannan kiraye-kiraye kuma ya yi abu mai kyau da ‘yan kasa za su ji dadi. Ya yi kyan kai kwarai,” shugaban na IPMAN ya jaddada.
3. Hakan na nufin dawo da tallafin fetur din ne?
Bayanan wadannan masu ruwa da tsaki za su bijiro wa da ‘yan Nijeriya da wata tambayar ta ko shin wannan sanarwa ta fadar shugaban kasa na nufin dawo da tallafin da aka cire ne?
Dr Adamu ya ce idan dai har shugaban kasa zai fito ya yi magana a kan daidaita farashi, tabbas hakan na nufin dawo da tallafi kenan.
“Idan dai har zai iya shigowa kasuwa ya hana farashi hawa ko sauka, to an dawo lokacin tallafi ne.
“Dama shi tallafi shi ne a daidaita farashi a tsayar da shi yadda gwamnati ke so. Cire tallafi kuma na nufin a bar kasuwa ta yi halinta.
“To idan kuwa har gwamnati za ta zo ta ce ga yadda za a sayar da mai to tallafi ya dawo kenan.
Duk da dai kungiyoyin dillalan man fetur ma suna da yakinin sanarwar shugaban kasar na yin inkari ne da mayar da tallafin, amma ba su da tabbacin iya kason da za a mayar.
“Ita kanta gwamnatin ta fadi hakan ne don sassautawa mutane zukatansu a tashin farko, amma akwai tarukan da za mu yi da yawa da wakilan gwamnati inda za a ji matsayin da gwamnatin za ta dauka.
“Sai an yi nazari an ga nawa za a kashe, me ya kamata a yi, sannan a tura wa majalisa don neman izininta tukunna,” a cewar Bashir Danmalam.
4. Mece ce alakar tashin dala da tashin farashin fetur?
A duk lokacin da gwamnati ta janye tallafin man fetur, hakan na nufin farashinsa zai dinga tashi a-kai-a-kai saboda ya ta’allaka ne kan sayo shi da dala da ‘yan kasuwa za su dinga yi.
“Cire tallafi dama a daidai wannan lokaci a Nijeriya zai yi wa kowace gwamnati wahala, ganin cewa matsalar da ake fuskanta ta dala ce tun da shigowa ake da tattacen fetur din kuma da dala ake sayensa,” kamar yadda kwararre kan harkar fetur Dr Adamu ya fayyace.
Ya kara da cewa: “Ita kuma dala ga shi sai kara hawa take yi. Kamar yadda duk rana farashin dala na yau da na gobe ba daidai yake ba, to shi ma haka farashin fetur zai dinga kasancewa.”
Shi ma Alhaji Danmalam ya ce “yanzu tun da an ce ‘yan kasuwa su je su shigo da wannan man kuma ku duba farashin canjin dala a kasuwar bayan-fage aid alar ta tafi kusan naira 1,000, to a haka idan ba a yi was aba sai an wayi gari farashin litar fetur din ma yah aura naira 1,000.
“A baya a kan farashin hukuma Babban Banki ke bai wa ‘yan kasuwa dalar inda ba ta wuce 420.
“Amma a yanzu babu wannan tsarin shi ya sa ta yi tashin gwauron zabi don dole ka saya a kasuwar bayan fage a kan sama da naira 900 ka kuma sayo man, ai kuwa idan ba a dau mataki ba dole abin ya shallake tunani.
5. Wa yake da alhakin daidata farashi?
Amsar wannan tambayar sai mu ce ta danganta ne da irin tsarin da ake ciki a kasar. Idan har an cire tallafi to ‘yan kasuwa ne suke da ikon juya akalar farashi, idan kuma akwai tallafi to ikon gwamnati ne ta daidaita farashi, a bayanin da Dr Adamu ya yi.
“Akwai hukumomin gwamnati masu kula da yanke farashin, amma a halin da ake ciki na yanye tallafi alhakin hakan na wuyan ‘yan kasuwa,” ya fada.
Alhaji Danmalam shi ma hakan ya fada inda ya kara da cewa “Kuma kowane dan kasuwa zai iya saka farashinsa daban, ya dangata da a kan nawa ya saro kuma a kan nawa ya canza dala, shi ya sa ake samun bambancin farashin litar mai a wurare daban-daban.”