Wata sabuwar doka da Majalisar Dokokin Jihar Bauchi a arewacin Nijeriya ta amince da ita ta yin amfani da harshen Hausa don gudanar da ayyukanta, ta zo wa mutane da dama da mamaki, ko da yake ta kayatar da dimbin mutane.
A ranar Laraba ne majalisar dokokin jihar ta sanar da cewa za ta dinga amfani da harshen Hausa a matsayin harshe na biyu na sadarwa a zaurenta bayan Turanci.
Hakan na nufin ‘yan majalisar za su dinga gabatar da kudurori da tafka muhawara da ma duk abin da ya shafi ayyukan zauren cikin harshen Hausa baya ga Turancin, wanda shi ne harshen da kasar take amfani da shi a hukumance.
Dan majalisar da ke wakilar karamar hukumar Shira, Honorabul Auwal Hassan, shi ne ya gabatar da kudurin a zamanta na farko da ta yi ranar Talata, 11 ga watan Yulin 2023.
Ya shaida wa TRT Afirka cewa ya yi hakan ne saboda a bai wa al’ummar da suka zabe su damar fahimtar abubuwan da ake gudanarwa a majalisar.
“Dama a tsarin dokar Nijeriya ta 1999 akwai sashe na musamman na 97 da ya ba da irin wannan dama, da kuma wata doka ta Majalisar Jihar Bauchi ta 3 a sashe na 8 da suka ba da damar cewa bayan Turanci, ana iya kara wani harshen da shi mafi yawan al’ummar jihar ke amfani da shi wajen sadarwa a zauren,” in ji shi.
Honorabul Hassan ya ce ganin cewa a Jihar Bauchi mafi yawan al’ummarta sun fi amfani da harshen Hausa “shi ya sa na gabatar da kudurin ta yadda wadanda suka zabe mu za su dinga sanin me ake yi a majalisar.
“Kuma mutane suna da damar zama da wakilansu wajen tabbatar da cewa sun aiwatar da abin da suka tura mu (wakilai) mu yi musu.
“Sannan hakan zai bai wa mutane da dama hanyar sauraron duk abin da majalisar ke yi, dama abin da muke son cimma kenan. Wannan mataki zai kara wa gwamnati da majalisar daraja don mutane su fahimci mun je wakilci ne da gaske ba dumama kujera ba,” a cewar Honorabul Hassan.
Me masana ke cewa?
Masana da dama na ganin wannan kuduri zai taimaka wajen saukaka sadarwa da kuma fahimta a ayyukan majalisa da mulki.
Sun ce wannan doka ta fito da gazawar da suka jima suna jawo hankalin jama'a game da ita a harkokin gudanarwar majalisun jihohi.
Aminu Makama Ilela, mai sharhi kan sha'anin siyasa da mulki kuma malami a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, ya ce yawancin wadanda ake zaba a matakin majalisar jiha ba su da ilimi na zamani mai zurfi da kwarewar aiki da za su yi magana da turanci a fahimce su kai-tsaye.
“Irin wadannan mutane kan je majalisar ba tare da sanin ayyukanta da kudurorinta ba, don haka idan aka kawo wata bukatar gwamnati a Turance ba ma fahimta suke yi ba.
“Mun ga yadda ko a kudu maso yammacin Nijeriya ma wasu jihohin suna amfani da Yarbanci a matsayin harshen sadarwa a majalisun dokokinsu.
“Hakan na da amfani don zai ba su dama su dinga fadar albarkacin bakinsu da bukatun al'ummominsu a cikin harshen da ya fi musu sauki, don wasu ba sa samun kwarin gwiwar yin magana da Turanci a zauren majalisa saboda gudun yin kuskure,” in ji masanin.
Shi ma Farfesa Aliyu Bunza, masani a harshen Hausa, ya ce wannan mataki na majalisar dokokin Jihar Bauchi ya yi matukar faranta ran masana harshe irin sa, saboda a ganinsa idan aka bari yara suka koyi ilimi da harshen-uwa ko aka yi amfani da shi a majalisa, to abu ne da zai kawo ci-gaba.
“Ta yaya za a ce ‘yan majalisar dokokin jihohi sun gudanar da yakin neman zabe da Hausa, sun yi dukkan mu’alamar neman kujerar da Hausa, amma sai an je batun wakiltar mutane sai a ce ba za a yi da harshen da mutanen da suka zabe su ke ji ba?” in ji Farfesa Bunza.
Amma kuma a bangare guda Malam Aminu Makama ya yi gargadin cewa kada ‘yan majalisar su saki jiki da amfani da Hausa zalla don gudun ka da lokacin da bukatar amfani da Turancin ta taso kuma su gaza saboda rashin gogewa.
Ta yaya za a ce ‘yan majalisar dokokin jihohi sun gudanar da yakin neman zabe da Hausa, sun yi dukkan mu’alamar neman kujerar da Hausa, amma sai an je batun wakiltar mutane sai a ce ba za a yi da harshen da mutanen da suka zabe su ke ji ba?
“Alal misali, idan nan gaba aka samu wasu hukumomi ko kasashe na duniya da ke son yin wata harka da Jihar Bauchi kan zuba jari ko ci-gaban jihar, kuma ya kasance ‘yan majalisun ne za su wakilci gwamnati wajen tattaunawar, to yaya abin zai kasance?
“Ko kuma ta yaya za a dinga nazarin kundin tsarin mulkin kasar ko na majalisar. Don haka ina kira ga ‘yan majalisa da kar su bari amfani da Hausar kuma ya zama wata katanga wajen gabatar da sauran al’amuran majalisar,” in ji Malam Aminu.
Karbuwar harshen-uwa a duniya
Baya ga kasashe irin na Afirka da Latin Amurka da yawanci suke amfani da harsunan kasashen-goyonsu, irin su Turanci da Faransanci da Sifaniyanci, sauran kasashen duniya suna amfani ne da harsunansu na kasa wajen gudanar da al’amura da dama.
Kuma masana na ganin hakan a matsayin wasu hanyoyi da suka kawo musu ci-gaba da ba su damar bunkasa ta wajen tafiya da zamani da kere-kere.
Kasashe irin su Turkiyya da China da Rasha da Azerbeijan da Iran duk suna amfani ne da harshe-uwa wajen gudanar da lamuransu kuma suna bunkasa, a cewar masana.
Hakan ce ma ta sa kwararru a fannin harshe irin su Farfesa Bunza, wanda malami ne Jami’ar Usman Danfodio ta Sokoto, ke ganin duk wanda aka haramta masa amfani da harshen-uwa to bai samu ilimi ba.
“Da a ce za a koma koyarwa da harshen Hausa a yankunan da ake amfani da harshen a Nijeriya da yaranmu sun ba da mamaki.
Ya jaddada cewa matukar kasashe irin Nijeriya ba a koma koyarwa da harshen-uwa ba to ba za a samu ci-gaba sosai ba.
Ya ba da misali da cewa ko a tsarin shari’a bai kamata a yi wa mutum shari’a da harshen da ba shi ne harshensa na uwa ba, “don ba lallai ya samu adalci yadda ya kamata ba.”