Darakta Janar na Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Nijeriya, wato National Intelligence Agency (NIA), Ahmed Rufai Abubakar, ya miƙa takardar ajiye aikinsa ga shugaban ƙasar Bola Tinubu ranar Asabar.
Da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan ya sauka daga muƙaminsa, Ahmed Rufai Abubakar ya ce ya ɗauki matakin ne don raɗin kansa.
Ya ƙara da cewa, "Akwai dalilai da dama da kansa mu ɗauki irin wannan mataki. Wasu na ƙashin kai ne, wasu na iyali. Amma dai ba abu ne muhimmi ba," in ji shi.
Ahmed Rufai Abubakar ya ce abotar da ke tsakanisa da Shugaba Bola Tinubu za ta ci gaba, yana mai cewa "na tattauna da shugaban ƙasa kuma ya fahimci dalilaina sosai kuma na yi alƙawarin ci gaba da taimakawa a fannin tsaron ƙasa."
Ya ce yana da ƙwarin gwiwa za a samu matasa da za su iya gudanar da harkokin ofishinsa, ganin cewa ya kwashe kusan shekaru bakwai yana horar da ma'aikata masu kaifin basira a hukumar.
Ya gode wa shugaban Nijeriya bisa ƙara masa wa'adi da ya yi na watanni 15 don gudanar da ayyukansa.
A shekarar 2018 shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya naɗa Ahmed Rufai Abubakar a kan muƙamin daga muƙamin babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin ƙasashen waje.