Ranar Larabar da ta wuce ne kamfanin mai na Nijeriya, NNPC Limited ya sanya hannu kan yarjejeniyar ciyo bashin gaggawa na dala biliyan uku daga bankin raya kasuwancin shiga da fitar da kayayyaki na Afirka, wato AFREXIM Bank.
TRT Afrika ya nemi karin haske kan bayanan mataimaki na musamman da ke bai wa shugaban Nijeriya shawara O'tega Ogra game batun.
1. Mene ne abin da rancen dala biliyan uku ya kunsa?
Kamfanin NNPC Ltd ya samo rancen gaggawa na dala biliyan uku daga Bankin AFREXIM da za a biya bashin ɗanyen mai da su.
Wannan yarjejeniyar ba ta ban-gishiri-in-ba-ka-manda ba ce, rancen tsabar kudi ne don a biya bashi da zai ba kamfanin damar cin gajiyar ribar danyen man da ake hakowa a Nijeriya.
Ga yadda abin yake dalla-dalla: a shekarun baya kamfanin NNPC yana ban-gishiri-in-ba-ka-manda da manyan kamfanonin da ke aikin hakar mai a Nijeriya.
Akwai basussukan da ake bin NNPC na ba-ni-gishiri-in-ba-ka-manda na danyen man fetur da tataccen man fetur.
Hakan ya faru ne saboda Nijeriya ta karbi tataccen man fetur da yawa daga kamfanonin man fetur da tunanin cewa nan gaba za ta biya su da danyen man fetur.
Labarin da za ku so ku karanta: NNPCL ya kama jirgin ruwa dauke da danyen mai na sata da za a kai Kamaru
Sai dai tuni aka dakatar da wannan tsarin, ga shi kuma Nijeriya ba ta kai ga gama biyan su da danyen man fetur ba.
Yanzu man fetur ya yi tsada a duniya, amma kasar ba ta cin moriyar haka saboda ko ta hako danyen mai tana amfani da shi ne wajen biyan wancan bashin.
Za a yi amfani da rancen bankin AFREXIM don biyan wancan bashin, abin da zai sakar wa NNPC Ltd mara, daga nan sai ta fara sayar da danyen man da ake hakowa a Nijeriya kai-tsaye wanda hakan kuma zai samar wa kasar daloli.
2. Wane amfani Nijeriya za ta samu daga rancen?
Kudin zai taimaka wa kamfanin NNPC Ltd wajen biyan bashi da haraje-haraje.
Kuma zai bai wa gwamnatin tarayyar kasar damar samun daloli wadanda za su taimaka wajen daidaita darajar naira.
3. Ta yaya za a rarraba kudin?
Za a raba kudin ne mataki-mataki bisa la'akari da bukatu da tanade-tanaden gwamnatin tarayya.
4. Shin rancen zai yi tasiri a kan farashin man fetur?
Idan naira ta farfado saboda wannan tsari da aka yi na rance, to hakan zai sa farashin man fetur ya sauka kuma hakan zai hana shi kara tashi a nan gaba.
5. Na san wani zai ce, ya batun tallafin mai, za a dawo da shi?
A'a. Idan naira ta samu daraja wannan zai sa farashin mai ya yi kasa wanda hakan zai sa ba a bukatar tallafin mai. Tsarin a bar kasuwa ta yi halinta yana nan bai sauya ba.
6. Ta yaya za a biya bashin?
Za a rika biyan rancen ne daga wani bangare na kudin da aka samu daga bangaren ribar da aka samu na danyen mai a nan gaba. Wani tsari ne don samar da daidaito tsakanin bukatun kasar kan tattalin arziki da harkar hako mai ta nan gaba.
8. Mene ne ya bambanta wannan da sauran yarjejeniyar ban-gishiri-in-ba-ka-manda na baya?
Wannan ba yarjejeniyar musayar danyen mai ba ce da tataccen mai wanda gwamnati ba ta samun riba daga ciki.