Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya gabatar da daftarin Sabon Shirin Cigaban Kasa mai dogon zango, wanda aka yi wa taken "Ajandar 2050", a fadarsa ta Aso Rock da ke Abuja babban birnin kasar.
Tun a watan Maris na wannan shekarar, Majalisar Mulkin Nijeriya ta amince da daftarin Ajandar 2050 wanda sai yanzu aka gabatar da shi ga jama’a.
Yayin da ake sa ran wannan kundi zai zama madubi ga gwamnatin kasar wajen tsara shirye-shiryen gina kasa, ga kudurorin shirin guda biyar da ya kamata ku sani.
1. Maye gurbin daftarin cigaba na 2020
Daftarin Ajandar 2050 zai maye gurbin kudurin cigaban Nijeriya na Vision 2020, da kuma Shirin Farfadowa da Habaka Tattalin Arziki na 2017-2020, wadanda da ma aikinsu ya kare a Disambar 2020.
Gabanin wannan daftari, Nijeriya ta fitar da Shirin Cigaban Kasa na 2021-2025, wanda asali shi aka shirya zai maye gurbin Kudurin 2020, da kuma Shirin Farfadowa da Habaka Tattalin Arziki na 2017-2020.
2. Habaka masana’antu a fadin kasa
Ajandar cigaba ta 2050, tana da burin kawo cigaban Nijeriya ta hanya habaka samuwar masana’antu da ilimin fasahar kere-kere, wanda za su zama kadarkon da za a assasa tattalin arzikin kasar.
Ministar Kudin Nijeriya ta bayyana cewa an tsara shirin Ajandar 2050 ne bayan lura da halin tattalin arziki da matsalolin jama’ar Nijeriya, da karancin cigaba, da rashin tsaro, da yawan jama’a, da kuma rashin fadadar tattalin arziki.
Ministar ta yi bayanin cewa a karkashin wannan shiri, mafi rinjayen zuba jari zai zo ne daga cibiyoyi masu zaman kansu. Matukar aka cimma wannan kuduri, to za a samu karuwar masana’antun samar da kayayyaki da ayyukan fasaha.
Sakamakon haka, an yi hasashen samun karin ayyukan-yi a Nijeriya da zai kai har miliyan 203.41 a shekarar 2050, wanda gagarumin kari ne idan aka kwatanta da adadin shekarar 2020.
3. Shiga sahun kasashe masu matsakaicin tattalin arziki
Kamar yadda fadar gwamnatin ta fada, shirin Ajandar 2050 yana da aniyar tabbatar da ganin Nijeriya ta cimma matakin da kowane dan kasa zai samar da kayayyaki a cikin gida, wanda za su kai kimar dala 33,328 duk shekara a ma’aunin GDP.
Wannan mataki zai sa kasar ta shiga sahun kasashe masu matsakaicin cigaban tattalin arziki a duniya, a dai wannan shekara ta 2050.
Ministar Kudi Zainab Ahmed ta sanar da cewa, ana hasashen a shekarar 2050 za a samu zuba jarin da zai kai kashi 40.11 na GDP, wanda zai haura na yanzu, wato 29.40.
Ana kuma sa ran rashin aikin yi a kasa zai ragu matuka, inda zai koma kashi 6.3% a shekarar ta 2050, daga kashi 33.3 a shekarar 2020. Idan wannan ya tabbata, talauci zai koma kashi 2.1% kacal a shekarar 2050.
4. Daidaiton cigaba tsakanin al’ummar kasa
Shugaba Buhari ya fada cewa, tun a yayin kafa kwamitin tsara wannan daftari ya nemi a tsara shirin da zai kunshi dukkan ra’ayoyi don tabbatar da daidaiton cigaba tsakanin al’ummomi da yankunan Nijeriya.
Kamar yadda Ministar Kudi ta bayyana, an tuntubi duka masu ruwa da tsaki da suka hada da ma’aikatun tarayya da cibiyoyin gwamnati da jihohi 36 da birnin tarayya da kuma wakilan kananan hukumomin kasar.
Akwai kuma kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin matasa da kungiyoyin kwadago da masarautun gargajiya da cibiyoyin addini da manyan jam’iyyun siyasa da kungiyoyin mata da kuma mutane masu bukata ta musamman.
5. Saukaka aiki ga gwamnati mai zuwa
Bayan kwashe tsawon shekaru takwas a mulki, gwamnatin Shugaba Buhari ta bayyana cewa wannan daftari zai taimaka wa gwamnati mai jiran gado wajen cika alkawuran da ta dauka ga ‘yan Nijeriya.
Dangane da wannan, daftarin ya kunshi kudurorin kafa dokokin da za su tabbatar da gudanar da aikin kaddamar da shirye-shiryen, ko da bayan karewar wa’adin gwamnatocin da za su zo nan gaba.