kungiyar Diamond Platnumz na daya daga cikin manyan tauraron mawaka a Afirka. Hoto: Getty

Daga Charles Mgbolu

Shahararriyar wakar nan mai suna "calm down" da fitaccen mawaki dan Nijeriya Rema ya rera, na kan ganiyarta bayan da ta fito a lamba ta daya a jerin wakokin da suka shahara a yankunan Gabas ta Tsakiya da arewacin Afrika (MENA).

Sama da mutum miliyan 380 ne suka saurari wakar ta farko a manhajar Spotify, yayin da mutum miliyan 700 suka kalli sabuwar wakar da ke nuna bidiyon mawakiya Ba'amurkiya Selena Gomez.

Selena ta ji dadin yadda ta shiga cikin wannan waka.

"Wannan mutumin ya sauya rayuwata har abada. Na gode Rema saboda zaba ta da ka yi na zama wani bangare na daya daga cikin wakoki mafiya shahara a duniya," in ji ta a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram.

"Idan ana son daukaka a fanni wake-wake a yau, dole sai a samu dimbin masu saurare a dandalin yada wakoki, wannan abu ne da ya zama wajibi," in ji Ade Adetunji, Shugaban Sashen Tallace-Tallace a kamfanin Audiomack Africa.

"Mataki ne babba ga mawaka saboda yadda aka shiga zamanin sauraro da kallon wakoki a intanet, babu wata hanya da ta kai kade-kade da wake-wake da za a keta yankunan duniya tare da yin tasiri a zukatan jama'a."

Mawakin Nijeriya Rema kenan yake wasan wakensa a yayin babban bikin kida na Roskilde 2023 a watan Yuni 2023./ Hoto: AFP

Al'adu Gama-Gari

Mawakan Afirka sun fara ganin tasirin yin amfani da intanet don yada wakokinsu cikin sauri. Burna Boy, Wizkid, Tems, Wally Seck (Sanagal), Sidiki Diabate (Mali), da kuma Diamond Platnum na daga cikin mawakan da za a iya lissafawa da suke da dimbin masu sauraro, kallo da bibiya a intanet.

"Da zarar wakokinku sun isa ga wajen kasashen da kuke, za ku yi tasiri kan al'adu gama-gari, ka zama mara iyaka ko kaidi," in ji Anthony Abrahams, Shugaban Sashen Nishadi a Gidan Talabijin na Silverbird da ke Nijeriya.

Ya kara da cewa "Wannan abu ne da mawakan kasashen Yamma suka dade da ganowa, kuma abu ne mai faranta rai yadda al'adu da muryoyin Afirka ke kara tasowa ta hanyar wadannan wake-wake."

Amma kasuwancin yada wakoki a intanet na bukatar daidaito tare da sabuntawa da kwarewa a koyaushe.

Mawakiya 'yar Afirka ta Kudu Zie Modinga kenan lokacin babban taron ba da lambar yabo na Afirka a 2021 a Lagos./Hoto: AFP

Amfani da manhajoji

Kwararru na bayyana cewa dole mawaka su rika kida da waka yadda za su karbu a matakin kasa da kasa muddin suna son manhajoji su karbi wakokin nasu.

"Dole ne su san yadda wakokinsu suke tashe a wasu yankunan na duniya domin samun damar fahimtar wadanne irin wakoki ne za su aika wa wadannan manhajoji."

Ya jaddada cewa "Hakan na nufin dole ne su fahimci yanayin mutanen da ke bibiyarsu don su rika rera wakokin da za su burge su."

Mawakiyar Tanzaniya da ta samu kyaututtukan karramawa da yawa Zuchi ta samu karin daukaka bayan fitar da wakarta mai suna 'Sukari' wadda sama da mutane miliyan 500 suka kalle ta a Youtube,

Hakan ya sanya ta zama mace ta farko da ta fi yawan samun masu kallon wakarta a tsakiyar Afirka.

Shi ma mawaki dan Nijeriya, Davido, kundin wakokinsa mai suna 'Timeless' ya kafa tarihi sosai, wanda a manhajar wakokin Apple ma a rana guda ya samu masu sauraro miliyan 7.25.

Tasiri

Rahoton 2023 da Tarayyar Wakokin Baka ta Kasa da Kasa (IFPI) ta fitar ya ce nahiyar Afirka ce ta fi samun habakar wakoki a shekarar 2022.

Drake na daga cikin fifattatun mawaka a masana'antar waka ta duniya./ Hoto: AP

Ofishin tattara bayanai na Satista ma sun yi hasashen bangaren wake-wake na Afirka zai samu dala miliyan 372.80 a 2023.

Mawaki dan Nijeriya Wizkid na da yawan masu sauraro biliyan 4.6 a Spotify. Yana daya daga cikin mawaka na kan gaba a Nijeriya.

Ya bunkasa wakokinsa bayan da ya hada gwiwa da mawakin Amurka Drake.

Bayan an saki wakar a manhajoji, ta samu shaidar Platinum ta Amurka bayan samun masu sauraro miliyan 9.1.

Adetunji ya ce "Wadannan alkaluma ne suke tasiri kan amo da sautin wakokin, da ma wajen samun kulla dangantaka da wasu."

TRT Afrika