Kamfanonin intanet da na sada zumunta da ke harkoki a Nijeriya sun biya naira tiriliyan 1.3 (dala biliyan 1.3) ga gwamnatin kasar a matsayin haraji a fiye da shekara daya, kamar yadda mahukuntan kasar suka bayyana.
Hukumar Kididdiga ta Kasar (NBS) ce ta wallafa alkaluman da ta samu daga Hukumar Tattara Haraji ta kasar wato Federal Inland Revenue (FIRS) a shafinta na intanet.
An karbi harajin ne daga kamfanoni kamar Google da Netflix da X (tsohon kamfanin Twitter) da kuma Meta daga watan Janairun 2022 zuwa watan Maris din 2023. Kudaden sun kunshi dukkan nau'ukan haraji ciki har da VAT.
A watan Yunin 2021, gwamnatin Nijeriya ta dakatar da kamfanin Twitter, wanda yanzu ake kira X, bayan kamfanin ya goge wani sako da Shugaban Nijeriya na lokacin Muhammadu Buhari ya wallafa a shafin.
An dage dakatarwar bayan wata bakwai bayan kamfanin sada zumuntan ya kulla wata yarjejeniya da gwamnatin Nijeriya, inda kamfanin ya sha alwashin sanya ido kan abubuwan da ake wallafawa a shafin da kuma yin rijista a Nijeriya da kuma sabon tsarin biyan haraji.
Yarjejeniya
A lokacin da gwamnatin kasar ta sanar da shirinta na fara karbar haraji daga kamfanonin intanet da ke aiki a Nijeriya.
Wadannan kamfanonin da suka kunshi wadanda suke yada bidiyoyi kai-tsaye da kamfanonin sada zumunta da kamfanonin da ke bayar da damar sauke abubuwa a intanet, an bukace su biya haraji ga hukumar karbar haraji ta kasar (FIRS).
Nijeriya ce kasar da ta fi karfin tattalin arziki a Afirka kuma ita ta fi yawan jama'a, har ila yau kasar tana samun bunkasar masu amfani da intanet.
Da taimakon intanet, kananan kamfanonin fasaha a kasar da kuma nahiyar suna taimakawa wajen samar da ayyukan yi da samar wa gwamnati kudin shiga da samar da masu zuba jari daga ketare.