| Hausa
Tinubu ya sha alwashin daukar mataki bayan kashe-kashe a Jos
01:11
Tinubu ya sha alwashin daukar mataki bayan kashe-kashe a Jos
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya umarci Rundunar Sojoji da Rundunar ’Yansandan ƙasa da su nemo tare da kama waɗanda ke da hannu a mummunan harin da aka kai Angwan Rukuba a Jos, Jihar Filato.
2 awanni baya

Haka kuma ya bayar da umarnin gaggauta girke kyamarori 5,000 masu amfani da fasahar Ƙirƙirarriyar Basirar wucin gadi (AI) domin ƙarfafa ayyukan tsaro a faɗin jihar.

Shugaban ya bayar da wannan umarni ne a ranar Alhamis yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a Jos, inda ya kuma jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu da kuma waɗanda suka jikkata sakamakon harin da ya yi sanadin mutuwar mutane 30 tare da raunata wasu da dama.

Ƙarin Bidiyoyi
Sojojin Isra'ila sun harbi wata yarinya a kai
Amurka da Isra'ila sun kai hari cibiyar makamai masu linzami na Iran
Sabon salo a siyasar Nijeriya: nazari kan jihar Kano
NASA ta kaddamar da tafiya zuwa duniyar Wata karon farko cikin shekara 50
Gwarazan da ke shiga kauyuka don yaki da HIV a Nijeriya
An yi kakkafar girgizar kasa mai maki 7.4 Indonesia
Kura mai launin ruwan goro da ta taso daga sahara ta lullube Tsibirin Crete na Girka
Atiku Abubakar ya ziyarci Rabiu Musa Kwankwaso a gidansa da ke Abuja
Yadda a-daidaita-sahu na 'mata zalla' ke sauya sufuri a birnin Kano
'Yansandan Isra'ila sun far wa yahudawa masu zanga-zangar adawa da hukuncin kisa