Masar ta yi nasara ta farko a tarihinta a gasar cin kofin duniya inda ta doke New Zealand da ci 3-1, lamarin da ya mayar da ita kan hanyar iya kai wa matakin sili ɗaya ƙwale a karon farko.
Mohamed Salah da Mostafa Zico da Trezeguet su ne suka ci wa Masar ƙwallaye, bayan Finn Surman na New Zealand ya fara zura ƙwallo a ragar Masar, minti 15 da fara wasan na rukuni G da aka yi a Vancouver.
Salah ya murnar cin ƙwallonsa ta 68 da ya ci wa ƙasarsa ta hanyar harba dunƙulallen hannsunsa cikin iska, kafin ‘yan tawagarsa su rufe shi a minti 67 da fara wasa, lamarin da ya sa magoya bayan tawagar Pharaoh sanye da jajayen riguna murna a filin wasa na BC Place da ya cika maƙil a Vancouver.
Lokacin da aka cire Salah bayan minti 85 da fara wasa, masu kallo sun tashi tare da yi masa tafi.
Masar ta koma saman teburi a rukuni na G da nasarar, amma ba ta samu tabbacin gurbi ba tukunna a matakin sili ɗaya ƙwale.
Masar za ta yi wasan da zai tantance matsayinta tare da Iran ranar Juma’a a Seattle, inda za ta buƙaci aƙalla canjaras domin ta iya zuwa mataki na gaba .
Finn Surman ne ya fara New Zealand a gaba minti 15 da fara wasa ta hanyar tashi sama da buga ƙwallo da kai bayan Tim Payne ya bugo kwana.









