A rana ta bakwai ta kalubalen rawa na dogon lokaci da yake yi shi kadai, Benjamin Daniel Gabriel ya ci gaba da rawa yayin da yake kokarin kafa wani sabon tarihin duniya a Najeriya— kasar da yin abubuwan ban mamaki domin samun suna a littafin Guinness ya zama wani abu da mutane ke yi don nishadi da kuma neman shahara.
Marayin, mai shekaru 32 wanda aka fi sani da "Ben Dancer," ya kuduri aniyar kafa sabon tarihi na rawa na dogon lokaci da mutum daya ke yi.
Ya zuwa ranar Talata, Gabriel — wanda ke rawa tare da mawaki Made Kuti, jikan fitaccen mawakin Afrobeat Fela Kuti—ya yi rawa ba tare da tsayawa ba na tsawon sa'o'i 176, mintuna 52 da dakika 59.
Tarihin yin rawa mafi dadewa da ake kai a yanzu, wanda ya kai sa'o'i 127, wata 'yar kasar India mai suna Srushti Sudhir Jagtap ce ta kafa shi a shekarar 2023, lokacin da take da shekaru 16 a duniya.
Gabriel shi ne mutum na baya-bayan nan a cikin jerin 'yan Najeriya da dama da suka taba kafa tarihi a duniya ko kuma suka yi kokarin yin hakan.
Kwanaki kadan bayan ya fara wannan kokari nasa, kimanin mutane 51,000 ne suka taru a Dandalin Tafawa Balewa da ke Legas — wurin da aka gudanar da bikin samun 'yancin kan Najeriya a hukumance, kusa da wurin da ake kira ‘Freedom Park’, inda Gabriel ke rawar—domin kafa tarihin kallon rawa mafi tara jama’a.
Hana kansa bacci
Yayin da wakokin Fela masu salon 'jazz' suka fara dusashewa, sai aka fara kunna wakokin Makossa masu kuzari na mawaki kuma mai buga ganga dan kasar Congo, Awilo Longomba; nan take Gabriel ya fara wani salon rawa mai cike da kuzari da sauri domin dacewa da yanayin sautin wakar.
Mutane da dama sun bi sahunsa wajen rera wakokin da kuma yin rawar.
A wani lokaci, dandazon mutanen ya fara bin salon motsin jikinsa yayin da ake ta kunna wakokin Afrobeats masu dauke da salon rawa da suka shahara a wurin taron.
"A gare shi, rawa abu ne mai alaka da ruhi," in ji mataimakiyarsa Mercy Idisi yayin da yake ci gaba da rawar.
"Kalubalen da muke fuskanta shi ne na bangaren tunani, musamman ma rashin samun isasshen barci."
Shirin Gabriel na wannan yunkuri na kafa tarihi a duniya ya fara ne tun a shekarar 2022, inda ya rika yin atisayen motsa jiki domin gina tsokoki, da horo na jure radadin ciwo da wahala, har ma da atisayen jure rashin barci domin shirya jikinsa yadda ya kamata.
Mako uku kafin ya fara wannan yunkuri, Gabriel ya samu matsala a gwiwoyinsa, lamarin da ya sanya masu shirya gasar cikin damuwa game da yadda hakan zai iya shafar burinsa.
Korafin lafiya
Sai dai bai fuskanci wata babbar matsalar lafiya ba a tsawon kwanaki bakwai na kalubalen rawar da ya yi, kamar yadda Chika Anagoba, likitar da ta kula da shi ta bayyana.
A gefen wurin da karamin taron mutanen ke rawa, mutanen asalin kauyen Gabriel a arewacin jihar Bauchi sun zauna a kan kujerun roba, suna cin abincin da ya shahara a Najeriya – shinkafar 'jollof' da hadin salak.
"Mun kasance a nan tun ranar farko," in ji Ibrahim yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na AFP. "Muna matukar alfahari da shi."
"Wannan yana nufin zan iya cim ma manyan abubuwa daga wurare masu sauki, kuma zan iya canza duniya ta hanyar rawa," in ji Gabriel ga AFP bayan kammala kokarinsa.
'Yan Najeriya sun nuna sha'awar gwada kafa sabbin tarihin duniya tun shekarar 2023, lokacin da Hilda Baci, mai girka shinkafar 'jollof', ta kafa tarihin yin girki na tsawon lokaci mafi tsawo da mutum daya ya taba yi.
Hukumar Guinness World Records ta bayyana cewa ta karbi bukatu kusan 1,500 daga kasar a watannin da suka biyo bayan kafa tarihin na Baci.
"Yan Najeriya ba sa zama na karshe a kowane fanni," in ji Tunde Onakoya, wanda ke rike da tarihin buga wasan 'chess' na tsawon lokaci mafi tsawo, yayin da yake zantawa da AFP a lokacin da Gabriel ke ta rawa a bayansa.
"A dabi'ance, 'yan Najeriya suna da jarumtaka da kuma son yin gasa sosai," in ji Onakoya.
"Muna son gwada kanmu a idon duniya don nuna cewa muna da ikon cim ma manyan nasarori iri-iri," in ji shi.
Sauran ‘yan Nijeriya da suka yi nasara
Sauran 'yan Najeriya da suka kafa tarihi sun hada da Helen Williams, wacce ta kera dogon gashin karya (wig) na hannu mai tsawon mita 351.28 (sama da ƙafa 1,152) a shekarar 2023, da kuma Munachimso Brian Nwana, wanda ya ziyarci gidajen cin abinci mai saurin dahuwa (fast food) guda 150 cikin sa'o'i 24—adadin da ya fi na kowa yawa, a cewar Guinness.
Gabriel ya nemi izinin Guinness World Records sau uku kafin a ba shi damar fara yunƙurinsa a watan Fabrairu.
Ya bayyana cewa ya fara rawa ne tun yana da shekaru 12 a matsayin hanyar kubuta daga matsin lamba na takwarorinsa da kuma matsalolin iyali, inda ya tilasta wa kansa koyon dabarun rawar har sai da ya samu damar samun horo na ƙwararru daga baya.
A lokacin wannan dogon aikin na rawa, ya riƙa cin abinci kaɗan tare da shan ruwan kwakwa, yayin da yake amfani da hutun minti biyar da aka amince a ba shi bayan kowace sa'a guda ta ci gaba da rawa; duk da haka, ya zaɓi ya tara lokacin hutun sannan ya yi rawa na tsawon sa'o'i da yawa a jere kafin ya ɗauki hutun nasa.
"Ina matuƙar alfahari da shi," in ji Onakoya, wanda shi ma ya kafa tarihin buga wasan dara (chess) na tsawon sa'o'i 60 a shekarar 2024.
Yayin da yake ci gaba da jiran tabbatar da tarihinsa a hukumance, tuni Gabriel ya fara shirin ɗaukar babban mataki wajen inganta al'adu da raye-rayen Afirka.
"Manufar neman shiga cikin tarihin Guinness World Records ba wai don kafa tarihin da kansa ba ne kawai," in ji shi.
"Manufar ita ce jawo hankalin duniya domin mutane su ƙara mayar da hankali kan raye-rayen asali na Afirka."






















