| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Ankara ta samar da shafin intanet kan taron COP31 na sauyin yanayi da za a gudanar a Turkiyya
Uwargidan shugaban ƙasar Turkiyya, Emine Erdoğan, ta sanar da ƙaddamar da sabon dandali na dijital na haɗin gwiwa a gabannin taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya COP31.
Ankara ta samar da shafin intanet kan taron COP31 na sauyin yanayi da za a gudanar a Turkiyya
Wannan dandali wani ɓangare ne na shirin Turkiyya don taron sauyin yanayi na COP31 / AA
5 awanni baya

Uwargidan shugaban ƙasar Turkiyya, Emine Erdoğan, ta sanar da ƙaddamar da sabon dandali na dijital na haɗin gwiwa a gabannin taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya COP31, inda ta ce manufarsa ita ce haɗa 'yan ƙasa, ƙungiyoyin farar-hula da masana'antu cikin tsarin diflomasiyyar yanayi na ƙasar.

A cikin wani sako da ta wallafa a ranar Jumma’a a shafinta na sada zumunta na Turkiyya, NSosyal, Erdoğan ta bayyana cewa “COP31 Digital Coordination Centre”, wadda Gidauniyar Zero Waste ta kafa, za ta samar da wuri na haɗin kai ga masu ruwa da tsaki waɗanda ba su cikin gwamnati don shiga cikin shirye‑shirye na taron da aka shirya gudanarwa a Antalya daga 9 zuwa 20 ga Nuwamba.

“Cibiyarmu ta 'COP31 Digital Coordination Centre' mallakin Gidauniyar Zero Waste ta haɗa muryoyin ƙungiyoyin farar-hula, ɓangaren masu zaman kansu da 'yan ƙasarmu a kan wannan dandalin guda,” in ji ta.

“Na yi matuƙar imani cewa wannan mataki mai ma'ana zai taimaka wajen tabbatar da cewa tsarin COP31 zai kasance mai ƙarfi, adalci kuma ya samu halartar mutane da yawa.”

Ta ƙara da cewa wannan cibiyar ta dijital za ta ƙarfafa mutane da hukumomin da ke wayar da kai kan muhalli su bayar da shawarwarinsu kuma su zama masu ruwa da tsaki a diflomasiyyar yanayi ta duniya.

Faɗaɗa aikin yaki da sauyin yanayi

Wannan dandali wani ɓangare ne na shirin Turkiyya don Taron Yarjejeniya na Majalisar Dinkin Duniya kan Sauyin Yanayi na Bangarori (COP31). Yana ba da bayanai game da taron COP da kuma hanyar da Turkiyya ke bi dangane da sauyin yanayi, tare da da hanyoyin da za su iya tallafa wa mahalarta taron a wurin taron.

Mutane da ƙungiyoyi za su iya mika ra'ayoyi, shawarwari da gudummawar ayyuka kai tsaye ta hanyar fom ɗin da aka samar a intanet a https://cop.sifiratikvakfi.org/.