| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Amurka da Iran na duba yiwuwar cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 45: Rahoto
Amurka da Iran suna tattaunawa don yiwuwar cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 45 da nufin hana ci gaba da ƙaruwar rikici, inda masu shiga tsakani ke mayar da hankali kan hanyoyin shiga Mashigar Hormuz da kuma tarin uranium ɗin Iran.
Amurka da Iran na duba yiwuwar cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 45: Rahoto
Rahotanni sun ce Amurka, Iran da masu shiga tsakani na yankin suna tattauna wa kan yiwuwar tsagaita wuta na tsawon kwanaki 45 / AP

Amurka da Iran da kuma wasu daga cikin masu shiga tsakani na yankin sun tattauna kan sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 45 wadda ka iya kawo ƙarshen yaƙin na har abada, a cewar kafar watsa labarai ta Axios.

Duk da cewa rahoton ya bayyana nasarar cim ma wani ɓangare na yarjejeniyar a cikin awanni 48 masu zuwa ba ta da yawa, amma yunƙurin ya kasance hanya ɗaya tilo da za a iya hana ƙaruwar rikicin.

Hakan zai haɗa da kai manya hare-hare kan kayayyakin more rayuwa na Iran da kuma ɗaukar fansa kan cibiyoyin samar da makamashi da ruwa a ƙasashen yankin Gulf.

Da farko dai, Shugaba Trump ya tsawaita wa'adin da ya ɗauka da cim ma yarjejeniya da Iran da awanni 20, inda ya ƙara wa'adin zuwa ranar Talata da ƙarfe 8 na dare agogon EST.

Masu AlakaTRT Afrika - Trump: Za a kai wa tashoshin lantarki da gadojin Iran hari idan ba a buɗe Mashigar Hormuz ba

Trump ya shaida wa Axios cewa Amurka "tana kan tattaunawa mai zurfi" kuma akwai yiwuwar a cim ma yarjejeniya.

"Akwai dama mai kyau, amma idan ba su cim ma yarjejeniya ba, zan lalata komai a can," in ji shi.

Yarjejeniyar matakai biyu

Rahotanni sun yi nuni da cewa, an gudanar da shawarwarin cim ma yarjejeniyar ne ta hanyar masu shiga tsakani daga Pakistan, Masar, da Turkiyya, da kuma saƙonnin kai-tsaye tsakanin jakada Steve Witkoff da Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi.

Yarjejeniyar matakai biyun da aka gabatar ta ƙunshi tsagaita wuta na kwanaki 45 sannan a kawo ƙarshen yaƙin na har abada.

Masu shiga tsakani sun yi imanin cewa sake buɗe Mashigar Hormuz da kuma warware batun uranium ɗin Iran zai iya kaiwa a har a cim ma yarjejeniyar ƙarshe.

'Yan Iran sun bayyana ƙarara cewa ba sa son "yanayin Gaza ko Lebanon" ya faru da su, inda a takarda ne batun tsagaita wuta ke wanzuwa kawai.

A halin yanzu, rundunar sojojin ruwan IRGC tana ci gaba da tsayin daka, inda ta bayyana cewa yanayin Mashigar Hormuz ba zai taba dawo wo zuwa yadda yake kafin somawar yaƙin ba.

Masu shiga tsakani sun jaddada wa jami'an Iran cewa babu wani arin lokaci na dabaru, domin awanni 48 masu zuwa suna wakiltar dama ta ƙarshe ta hana ɓarna mai yawa.

Rumbun Labarai
Mene ne Tehran ke gabatarwa domin kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran?
Araghchi ya faɗaɗa zirga-zirgar diflomasiyyar Iran daga Islamabad zuwa Moscow
Sisi na Masar ya yi gargaɗi kan 'ƙoƙarin da ake yi da gangan' na sake zana taswirar Gabas ta Tsakiya
Falasɗinawa na kaɗa ƙuri'a a zaɓen farko tun bayan yaƙin ƙare-dangi da Isra'ila ta ƙaddamar a Gaza
Iran ta ce ba kai-tsaye za a yi tattaunawa a Pakistan don kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra’ila ba
Turkiyya da ƙasashe bakwai sun soki Isra'ila kan keta alfarmar Masallacin Ƙudus
Trump ya fasa kai wa Iran hari da makamin nukiliya
Daraktan IEA ya ce ana asarar gangar mai miliyan 13 kullum saboda rufe Mashigar Hormuz
Amurka ta dakatar da jigilar dala zuwa Iraƙi, amma me ya sa take aika kuɗi zuwa Baghdad?
Trump ya tsawaita tsagaita wutar Iran domin bai wa Tehran ƙarin lokaci na tattaunawa
Vance zai tafi Pakistan ranar Talata domin tattaunawa da Iran  — rahoto
Sojan Isra’ila na shan suka bayan ya lalata mutum-mutumin Yesu a Lebanon
Iran ta kai harin ramuwar gayya kan jiragen Amurka a kan ƙwace jirgin dako: Rahoto
Isra'ilawa da dama sun mamaye Masallacin Ƙudus a ƙarƙashin rakiya da tsaron 'yansanda mai tsanani
Trump ya ce Amurka na yin tattaunawa mai kyau da Iran, ya yi gargaɗi kan rufe Mashigar Hormuz
Hare-haren Iran sun lalata fiye da gidaje 1,000 tare da mayar da su kufai a Tel Aviv - Magajin Gari
Iran ta kama mutum 127 kan zargin taya abokan gaba shirya kai mata hari ta ƙasa
Trump ya ce za a yi amfani da ‘manyan katafilolin tone kasa’ don kwashe sinadarin Uranium daga Iran
Iran ta sanar da bude Mashigar Ruwa ta Hormuz ga dukkan jiragen ruwan duniya
Jakadan Iran a MDD ya bayyana ƙawanyar Amurka a matsayin 'matakin tsangwama'