| Hausa
TURKIYYA
3 minti karatu
Turkiyya ta yi Allah wadai kan girmama Ratko Mladic da aka yanke wa hukuncin laifin yaƙi
Ankara ta ce girmama tsohon kwamandan Serbia yana ƙara wa waɗanda abin yaƙin baya ya shafa raɗaɗi kuma yana rage ƙoƙarin da aka yi na shekaru da dama na samar da zaman lafiya da sulhu a yankin Balkans.
Turkiyya ta yi Allah wadai kan girmama Ratko Mladic da aka yanke wa hukuncin laifin yaƙi
Turkiyya ta yi Allah wadai da girmama Ratko Mladic da aka yanke wa hukuncin laifin yaki

Turkiyya ta yi Allah wadai da mutane da ke amfani da mutuwar Ratko Mladic a matsayin wata dama ta yabo da jinjina duk da cewa an same shi da laifukan yaƙi masu tsanani.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta ce kotunan duniya sun yanke wa Mladic hukunci kan kisan ƙare-dangi da laifukan cin zarafin bil'adama da kuma laifukan yaƙi, kana ta yi gargaɗin cewa ƙin amincewa da waɗannan hukunce-hukuncen ko ɗaukaka waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa yana ƙara wa waɗanda abin ya shafa da iyalansu ƙunci.

Ankara ta yi kira da a ɗauki darussa daga baya

Ma'aikatar ta ce yabo ko kuma ƙoƙarin girmama Mladic na gurgunta shekarun da aka kwashe ana aiki don samar da zaman lafiya da sulhu a yankin Balkans.

"Abin da Balkans ke buƙata shi ne gina makoma mai cike da zaman lafiya da wadata da kuma rayuwa mai kyau, wadda ake bi bisa darussa da aka koya a baya," in ji ma'aikatar.

Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Hague ta yanke wa Mladic, wanda aka fi sani da "Mahaucin Bosnia," hukunci ne kan rawar da ya taka a mummunar ta'asar da aka aikata a lokacin yaƙin Bosnia na 1992 zuwa 1995, gami da kisan kiyashin Srebrenica na 1995.

Ya mutu a ranar 27 ga watan Agusta yayin da yake zaman ɗaurin rai-da-rai a Hague, daga baya ne aka kai gawarsa Belgrade, inda aka karɓe shi da girmamawa ta soja kafin a binne shi a ranar Litinin.

Dubban mutane sun halarci jana'izar, ciki har da jami'an Serbia, lamarin da ya jayo suka daga ƙasashen duniya.

Kazalika lamarin ta janyo tsamin dangantakar tsakanin Serbia da Tarayyar Turai.

Kwamishinar Faɗaɗa Tarayyar Turai Marta Kos ta soke ziyarar da ta shirya kai wa Serbia, tana mai cewa ɗaukaka Mladic bai dace da ƙa'idodin da ke ƙarƙashin tsarin ƙasar na shiga ƙungiyar Tarayyar Turai ba.

Turkkiya ta girmama waɗanda suka rasa rayukansu a Yaƙin Bosnia

Ma'aikatar Harkokin Waje ta Turkkiya ta kuma yi wa waɗanda aka kashe a lokacin Yaƙin Bosnia, musamman waɗanda aka yi wa kisan kiyashi na Srebrenica ta’aziyya tare da nuna goyonta baya ga iyalansu.

Ma'aikatar ta ce, sake tuna abubuwan da suka faru a baya da mutunta waɗanda abin ya shafa da kuma ƙin girmama waɗanda aka yanke wa hukuncin laifukan yaƙi suna da mahimmanci wajen gina zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Balkans.

Kalaman gwamnatin ƙasar na zuwa ne a daidai lokacin da batun jana'izar Mladic ya tayar da muhawara kan yadda Serbia da yankin baki daya ke tuna yakin Bosnia da kuma laifukan da kotunan duniya suka kafa.