Turkiyya ta bayyana cewa Iran na fuskantar “hari na zalunci kuma ba bisa ka’ida ba”, tana mai Allah-wadai da hare-haren da Amurka da Isra’ila ke kai wa, tana mai cewa ba su da wani halacci a karkashin dokokin kasa da kasa.
Da yake magana a wani taron manema labarai a Ankara ranar Litinin, kakakin jam’iyyar AK, Ömer Çelik, ya ce harin kan Iran “zalunci ne, ya saba wa dokokin kasa da kasa kuma ba shi da wani halacci.” Ya yi gargadin cewa kai hare-haren soji yayin da ake ci gaba da tattaunawar diflomasiyya na iya haifar da “mummunan sakamako mai tayar da hankali.”
“Ba za a iya amfani da diflomasiyya a matsayin rufa-rufa ga hare-haren da aka riga aka tsara ba,” in ji shi. “Idan ana cikin tattaunawa kuma aka kai irin wannan hari, hakan na aika sako cewa tattaunawar dabara ce kawai.”
Çelik ya mika ta’aziyya ga al’ummar Iran kan rahotannin asarar rayukan fararen hula, ciki har da harin bam kan wata makarantar firamare, da kuma mutuwar manyan shugabannin addini, soji da na siyasa. “Iran na karkashin hari na zalunci kuma ba bisa ka’ida ba,” in ji shi, yana mai kira da a gaggauta komawa teburin tattaunawa.
Barazana ga daukacin yankin
Ya yi gargadin cewa kai hari kan shugabancin wata kasa mamba a Majalisar Dinkin Duniya da kuma bayyana batun sauya gwamnati a fili zai kara dagula yankin. Ya ce kokarin kakaba sauyin gwamnati a tarihi ya kan jawo yakin basasa da kuma dogon rikici.
“Tsoma bakin da ake yi da sunan tsaron Isra’ila ko kuma domin goyon bayan tsattsaurar ajandar manufofin harkokin waje na Isra’ila ya dagula daukacin yankin,” in ji shi, yana mai cewa tsarin kasa da kasa na bayan Yaƙin Duniya na Biyu na fuskantar barazanar rushewa.
Yayin da yake nuna goyon baya ga al’ummar Iran, Çelik ya kuma gargadi Tehran da kada ta fadada rikicin ta hanyar kai hari kan wasu kasashe na uku.
“Dole ne a rarrabe a fili tsakanin hakkin kare kai da kuma matakan da za su iya jawo yakin yanki mai fadi,” in ji shi.
Ya kara da cewa Ankara na sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa tare da shirya matakai daban-daban, ciki har da yiwuwar rikicin ya bazu a yankin.
Ya ce hukumomin Türkiyya na daukar matakan kariya a fannoni hudu masu muhimmanci: yiwuwar kwararar ‘yan gudun hijira daga kan iyakar Iran, rikicewar tattalin arziki da ke da nasaba da hanyoyin makamashi kamar mashigar ruwan Hormuz, shirin tsaron kasa, da kuma amincin ‘yan kasar Turkiyya da ke kasashen waje.
“Hukumominmu na aiki cikin cikakken hadin kai,” in ji Çelik, yana mai cewa ofisoshin jakadanci na aiki dare da rana domin taimaka wa ‘yan kasar Turkiyya da ke son barin kasashen da rikicin ya shafa.
Amurka da Isra’ila sun kaddamar da hari kan Iran ranar Asabar, inda suka kashe manyan shugabannin Iran da dama, ciki har da Jagoran Koli, Ali Khamenei.
Tehran ta mayar da martani da jerin hare-haren jiragen yaki marasa matuki da makamai masu linzami, inda ta kai hari kan Isra’ila, kadarorin Amurka, da kuma wasu kasashen yankin Tekun Fasha.

















