Yadda goyon bayan Falasɗinu ya haɗa kan Musulmai suka goyin bayan Spain a Gasar Kofin Duniya na 2026
WASANNI
3 minti karatu
Yadda goyon bayan Falasɗinu ya haɗa kan Musulmai suka goyin bayan Spain a Gasar Kofin Duniya na 2026Game da Gabas ta Tsakiya, masu goyon bayan Sifaniya suna kallon ta tamkar wakiliyar Falasdinawa, yayin da Argentina kuma ake mata kallon wadda ke mara wa Isra’ila baya.
Argentina Spain WCup Soccer

Nasarar da Sifaniya ta samu kan Argentina da ci 1-0 a wasan karshe na Gasar Kofin Duniya ta fito da yadda siyasa da rikicin Gabas ta Tsakiya suka jawowa kasar Argentina bakin-jini tun daga fara gasar.

Game da Gabas ta Tsakiya, masu goyon bayan Sifaniya suna kallon ta tamkar wakiliyar Falasdinawa, yayin da Argentina kuma ake mata kallon wadda ke mara wa Isra’ila baya.

Misali, wasu Falasdinawa da ke wani sansanin ’yan gudun hijira a Gaza, sun yi ta murna da shewa bayan da Sifaniya ta samu wannan nasara kan Argentina, tamkar nasarar Sifaniya, nasararsu ce.

Kazalika, shafin X na hukumar kasar Falasdinu ya wallafa sakon taya Sifaniya murna, inda ta sanya alamar tutar Falasdinu da ta Sifaniya, tare da hoton tawagar Sifaniya yayin da suke murnar nasarar lashe Kofin Duniya.

Mece ce alakar Sifaniya da Falasdinawa? Bari mu dan waiwayi tarihi kadan.

Goyon bayan da Sifaniya take nuna wa Falasdinawa a hukumance ya samo asali ne tun watan Satumbar shekarar 1979, lokacin da Sifaniya ta zama kasa ta farko a Yammacin Turai da ta karbi bakuncin Shugaban kungiyar Falasdinawa ta PLO, marigayi Yasser Arafat.

Kazalila Sifaniya ta ci gaba da nuna goyon baya ga Falasdinawa har zuwa lokacin da ta amince da kasar Falasdinu a hukumance ranar 28 ga watan Mayun 2024.

A daya bangaren kuma, a hukumance Argentina ta fara bai wa Isra’ila goyon baya ranar 31 ga Mayun 1949, shekara guda bayan Isra’ila ta shelanta ’yancin-kanta. Argentina ta amince da Isra’ila sannan ta fara huldar diflomasiyya da ita.

Gabanin wasan karshen na Kofin Duniya, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana goyon bayansa a fili ga Argentina, har ma jakadan Argentina a Isra’ila ya ba shi kyautar jesin Argentina.

Sannan wani abu da ya kara siyasantar da wasan karshen shi ne batun kyaftin din Argentina, Lionel Messi, wanda ake zargi da nuna goyon bayansa ga Isra’ila, har ake nuni da ziyarar da Messi ya kai birnin Kudus, inda ya yi addu’a a bangon Yamma, wato Western Wall sanye da hular- ƙeyar nan ta Yahudawa, tare da wata tawagar ’yanwasan kungiyar Barcelona a shekarar 2013.

Wasu na kwatanta Messi da Lamine Yamal na Sifaniya, wanda Musulmi ne da ke bayyana goyon bayansa a fili ga jama’ar Falasdinu. An sha ganin Yamal wanda mahaifinsa dan asalin Morocco ne, yana daga tutar Falasdinu, misali bayan lashe Kofin La Liga a watan Mayun bana.

Wani abu da ya kara wa Sifaniya farin-jini shi ne rashin jituwar siyasa da yake tsakaninta da Amurka, wadda ita ce babbar aminiyar Isra’ila kuma a kasar da aka buga wasan karshen, wanda ya samu halartar Shugaba Donald Trump.

Ita kuma Argentina ta kara samun bakin-jini musamman ga masu kishin daidaita launin fata da suke sukar cewa tawagar Argentina ba ta da danwasa bakar fata ko daya, duk da akwai bakaken fata a kasar tsawon daruruwan shekaru.