Gwamnatin Nijar ta cim ma wata yarjejeniya ta haɗin gwiwa tsakaninta da wani kamfani mai zaman kansa da kuma Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Nijar (NEPP) don gina tashar samar da wutar lantarki ta hasken rana mai ƙarfin megawatt 200 tare da adana batura, a cewar rahoton kamfanin dillacin labarai na Nijar.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, kamfanin mai zaman kansa ne zai gina tashar tare da gudanar da ita tsawon shekaru 20 kafin ya miƙa ta ga gwamnatin Nijar.
Kazalika za a sayar da wutar lantarkin da ake samarwa daga tashar ga kamfanin NIGELEC na ƙasa, a kan CEFA 35 kan kowane kilowatt.
Ana sa ran kammala ayyukan gina tashar a watanni 24, a cewar shugaban kamfanin NEPP.

Gwamnati ƙasar ta ce aikin zai taimaka wajen wadatar da gidaje da cibiyoyin gwamnati da ‘yan kasuwa wutar lantarki, tare da rage dogaron Nijar kan wutar lantarki daga ƙasashen ƙetare.
A halin da ake ciki, Nijar ta dogara ne da shigowa da wutar lantarki mai yawa daga maƙociyarta Nijeriya.
Jami'ai sun ce ƙara yawan hanyoyin samar da wutar lantarki da ke amfani da hasken rana zai taimaka wa Nijar wajen inganta tsaron makamashinta da kuma rage dogaro da shigo da wutar lantarki daga waje.
Kazalika ƙasar ta ƙuduri aniyar sabunta hanyoyin samar da wutar lantarki musamman daga hasken rana da kuma iska, wanda zai samar da kashi 30 cikin 100 hanyoyin wutar lantarki daga yanzu zuwa shekarar 2030.


















