Rundunar 'yansandan jihar Legas a Nijeriya ta kama wasu 'yanƙasashen waje su 38 a yankin Epe na jihar, bayan rahotannin sirri da ta samu game da kasancewar dimbin baƙi 'yankasashen waje da ke zama a wani gini a yankin.
Kwamishinan 'yansandan jihar Legas, CP Fatai Tijani ne ya ya bayyana cewa an fara aikin ne bayan da bayanan sirri suka nuna cewa akwai wasu ayyukan da ake zargi da suka shafi mazauna ginin.
Waɗanda aka kama sun hada da ‘yan China 14 da ‘yan Kamaru 9, sai kuma 'yan Benin 4, da 'yan Malaysia hudu, da 'yan Togo biyu da kuma mutum ɗaya ɗan Ghana. a cewar kwamishinan ‘yansandan.
Kazalika ya yi kari da cewa, ‘yanƙasashen wajen da aka kama ba su da alaƙa da bidiyon mutanen da aka yi ta yaɗawa a kwanan nan a shafukan intanet.
Kwamishinan ya ce binciken farko da aka gudanar ya gano cewa, mutum 20 daga cikin wadanda ake zargin sun shiga Nijeriya ba bisa ka'ida ba, yayin da 18 kuma sun mallaki shedar fasfo tafiya na ECOWAS.
Haka kuma mafi yawa daga cikinsu ba su ba da gamsarsun bayanai game da ayyukan da suke yi a Nijeriya ba.
Ya kuma ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargin sun yi iƙirarin suna gudanar da harkokin kasuwanci ne ta intanet amma ba su iya bayyana yadda suke gudanar da ayyukan ba.
Tuni dai aka tura shari'ar zuwa ga Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya da ofisoshin jakadancin kasashen mutanen da abin ya shafa don ci gaba da bincike.










