'Yan Nijar na fama da karancin takardun kudi

'Yan Nijar na fama da karancin takardun kudi

Al’ummar Jamhuriyar Nijar na ci gaba da jin radadin takunkuman da ECOWAS ta sanya wa kasar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum. ECOWAS ta dauki jerin matakai, ciki har da rufe iyakokinta da Nijar da kuma daina duk wata hulda da ita, bayan juyin sojoji sun kifar da gwamnatin dimokuradiyya a watan Yulin da ya gabata.