Katse wutar lantarki a Nijar ya sa amfani da janareto

Katse wutar lantarki a Nijar ya sa amfani da janareto

'Yan kasar Nijar sun mayar da hankali wurin amfani da janareto sakamakon katsewar lantarki bayan ECOWAS ta kakaba wa kasar takunkumai. Nijar tana samun fiye da kashi 70 cikin dari na wutar lantarkinta daga Nijeriya amma makwabciyar tata ta katse lantarkin bayan sojojin da suka yi wa Mohamed Bazoum juyin mulki sun ki mayar da shi kan mulki.