Rikicin juyin mulki a Nijar

Rikicin juyin mulki a Nijar

Ana sa ran shugabannin rundunonin soji daga kasashen Yammacin Afirka za su gana don duba yiwuwar daukar matakin soji kan sojojin da suka hambarae da Shugaban Kasar Nijar Mohamed Bazoum a makon da ya gabata. Wannan ya biyo bayan taron musamman da shugabannin ECOWAS suka gudanar a Abuja babban birnin Nijeriya. Shugabannin yankin sun sha alwashin daukar matakin da ya dace.