Bunkasar cibiyoyin sauya motoci daga fetur zuwa gas a Abuja
Yayin da gwamnatin Nijeriya ke jan hankalin 'yan ƙasar masu motoci su rungumi amfani da gas wanda ake matse shi a matsayin makamashi maimakon amfani da man fetur, wanda farashinsa yake ƙara tashi, a yanzu haka kamfanoni masu zaman kansu suna buɗe wuraren da ake sauya motoci daga masu amfani da fetur zuwa masu amfani da gas wato CNG.
A ziyarar da TRT Afirka Hausa ta kai Nijeriya a baya-bayannan, mun kai ziyara ɗaya daga wuraren da ake buɗewa a babban birnin ƙasar, Abuja