Bosphorus: Ruwan da ya raba nahiyar Turai da Asiya a Istanbul

Bosphorus: Ruwan da ya raba nahiyar Turai da Asiya a Istanbul

Mashigar ruwan Bosphorus da ke birnin Istanbul na Turkiyya na cikin manyan mashigun ruwa na duniya. Hanya ce ta teku da ke hada sassan duniya da dama. Mashigar tana kewaye da manyan wuraren tarihi irin su masallatai da gidajen adana kayan tarihi da fadojin manyan sarakuna na zamanin da. Sannan mashigar Bosphorus ita ce ta hada yankin Turai da Asiya da ke zama hanyar kasuwanci, kuma masu yawon bude ido sukan ziyarce ta domin kashe kwarkwatar idanunsu, kamar yadda za ku gani a wannan rahoto.