Bello Turji bai gagare mu ba - Ministan Tsaron Nijeriya
Ministan Tsaron Nijeriya Muhammad Badaru Abubakar ya ce an yi matukar samun ci gaba a fannin tsaro cikin shekara guda da fara mulkinsu, “sakamakon jajircewar sojoji da goyon bayan da gwamnonin jihohi ke bayarwa.”
A wata hira ta musamman da ya yi da TRT Afrika Hausa, Ministan Tsaron ya yi magana kan batutuwa da dama ciki har da martani kan zargin da ake cewa ba a biyan sojojin kasar hakkinsu yadda ya kamata da kuma zancen kama Bello Turji.