Ba na so na samu matsala a Kannywood har lokacin da zan yi aure - Ma'u ta Fim ɗin Garwashi
‘Yar wasan Kannywood ɗin nan wadda tauraruwarta ke haskawa Nana Fiddausi Yahaya wadda aka fi sani da Asmau a shiri mai dogon zango na Garwashi ta shaida wa TRT Afrika Hausa yadda ta tsinci kanta a harkar fim da kuma wasu nasarori da ta samu.