Amfanin shuka bishiya don rage zafin duniya

Amfanin shuka bishiya don rage zafin duniya

Ko kun san cewa duk da tsananin zafin da muke yawan kuka a kansa da yake samuwa ta dalilin zafin rana, tazarar da ke tsakaninmu da ranar nan ta kai tafiyar shekara 3,536 idan da ƙafa za a je? Masana sun ce ba komai ke sa muke jin tasirin zafin ranar ba sai irin yadda ɗan’adam ke lalata duk wata kariya daga zafin rana da Ubangiji ya saukar mana a duniya, kamar sare bishiyoyi. A wannan bidiyon, Halima Umar Saleh ta yi mana nazari kan abin da ya kamata mu yi don ceto duniya daga tsananin zafi.