ADLaM: Tsarin rubutun Fulatanci

ADLaM: Tsarin rubutun Fulatanci

Fulani na daya daga cikin manyan kabilun da ke zaune a Yammaci da Tsakiyar Afirka. Sai dai ta kwashe shekaru aru-aru ba tare da tsarin rubutunta ba sai kwanan baya da wasu 'yan uwa biyu daga kasar Guinea suka kirkiro tsarin. Abdoulaye da Ibrahima Barry sun ce tsarin rubutun zai taimaka wa harshen Fulatanci da kuma inganta tsarin sadarwa da iliminsu.