Abin da ya kamata ku sani game da fari

Abin da ya kamata ku sani game da fari

A shekarun baya-bayan nan, fari ya janyo iftila'o'i a kasashe da dama na duniya wanda ke shafar mutane da yawa, dabbobi da ma muhalli. Alal misali, a Ethiopia, Somalia da wani bangare na Kenya, kusan mutane miliyan 32 na gwagwarmaya da tasirin fari da yake-yake a lokaci guda, ga kuma karancin abinci da cututtuka da ke addabar su, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar. To, mene ne fari?