Ɗan shekara 17 ya ƙirƙiro na’ura don taimaka wa makafi a Kano
Wani yaro dan sakandare mai shekara 17 ya ƙirƙiro wata na’ura da nufin taimaka wa makafi yin tafiya ba tare da sun yi amfani da sanda ba. Matashin ya ce yana manufarsa ita ce sauƙaƙa wa makafi wahalhalun tafiya da kuma kauce wa haɗarurruka. Baya ga na’urar taimaka wa makafi, matashin ya ce ya ƙirƙiro abubuwa da dama da suka haɗa da na’urar gano bam da wasu abubuwan.