‘Na kera jirgi amma ban taba shiga aji ba’
Malam Hadi Usman wani dattijo ne da bai taba zuwa makarantar boko ba, amma kuma ya samu ya kera jirgin helikwafta da wayar salula da sauransu.
Jami’ar jihar Gombe ta karrama dattijon da digirin girmamawa a fannin kimiyya da fasahar kere–kere a farkon watan Oktoban 2023.