Zabukan da aka gudanar a jihohin Kogi da Imo da Bayelsa na Nijeriya a ranar Asabar sun bar baya da ƙura sakamakon fatali da sakamakonsu da jam'iyyun hamayya suka yi.
A Jihar Kogi, an ayyana Ododo na APC a matsayin gwamna inda ya samu ƙuri’a 446,237 daga cikin jumullar ƙuri'un da aka kaɗa 791, 890.
Sai dai ƴan takarar SDP Murtala Ajaka da na PDP Dino Melaye duk sun yin watsi da shi.
Can a Jihar Imo da ke kudu maso gabashin Nijeriya ma hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar INEC ta ayyana Hope Uzodimma na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri'a 540, 308.
Amma da sanarwar hakan sai wakilan jam'iyyun adawa da ke wajen suka ruɗe da hayaniyar cewa ba su yarda da zaɓen ba saboda sakamakon "bai yi daidai da abin da suka shaida a rumfuna ba."
A Jihar Bayelsa kuwa ba a kai ga sanar da wanda ya lashe zɓen ba tukunna, saboda ɗaga tattara sakamakonsa da INEC ta yi zuwa yau Litinin da rana.
Sai dai tuni INEC din ta sanar da karɓar sakamakon ƙananan hukumomi shida daga cikin takwas na jihar.
Jam'iyyu 16 ne suka tsayar da ƴan takara a zaɓen na Bayelsa, amma fafatawa ta fi zafi ne tsakanin Gwamna Duoye Diri na PDP da tsohon Ministan Man Fetur kuma tsohon gwamnan jihar, Timipre Sylva na APC.
Ga alama watsi da sakamakon da jam'iyyun da ba su yi nasara ba suka yi na nuna wataƙila sai an dangana da Kotun Sauraron Kararrkin Zabuka, wadda ba ta dade da kammala yanke hukunci a kan zabukan wasu jihohin ƙasar da aka yi a watan Maris din shekarar da muke ciki ta 2023 ba.
Sannan har yanzu Kotun Daukaka Karar da Kotun Koli ba su kai ga yanke hukuncin ƙarshe kan hukunce-hukuncen farko na Kotun Karararkin Zaben ba.
Wani labari mai alaƙa: Amsoshin tambaya shida kan Kotun Sauraron Kararrakin Zabe ta Nijeriya
Waɗannan zaɓuka na jihohi uku da aka yi ranar Asabar sun ɗauki hankulan ƴan Nijeriya sosai, in da suka kasance daga cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a kansu a shafukan sada zumunta tun daga ranar Asabar har zuwa wayewar garin Litinin.
Maudu'ai irin su #KogiDecides #2023 da #Dino, wato dan takarar PDP na Jihar kogi Dino Melaye da kuma #INEC sun yi ta tashe a shafin X.
Dino Melaye a Kogi
Duk da cewa za a iya cewa sunan Sanata Dino Melaye fitacce ne sosai ba a Jihar kogi ba har ma a fadin Nijeriya, musamman ganin yadda sunansa ke cikin maudu'an da suka fi tashe a kwanakin nan, to sakamakon zaɓen ya nuna shi ya zo na uku da jam'iyyarsa ta PDP da ƙuri'a 46,362, yayin da ɗan takarar SDP ya yi na biyu da ƙuri'a 259,052.
A wani taron manema labarai da ya kira a Lokoja ranar Lahadi, Melaye ya yi watsi da sakamakon tare da yin kira kan soke shi gaba ɗaya.
“Dole ne INEC ta soke zaɓen nan. Muna da hujjojin da za mu nuna, INEC ta nuna rashin ƙwarewa, ba za a iya yarda da ita ba, ta nuna son kai ta kuma saɓa ƙa'ida," ya ce.
A Jihar Imo ma ɗan takarar Jam'iyyar Labour Party Achan Achonu ya yi watsi da sakamakon, yana cewa zai garzaya kotu don ƙalubalantarsa.
Mr Achonu ya faɗi hakan ne a ranar Lahadi yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a ƙauyensa da ke Umulomo a ƙaramar hukumar Ehime Mbano.
Ya yi zargin cewa an "tafka maguɗi" a zaɓen ciki har da sayen ƙuri'u da ma dukan wakilan jam'iyyarsa, don haka ya yi kira da "a soke zaɓen gaba ɗaya."