Yarima Harry da matarsa Meghan sun isa Nijeriya don halartar Wasannin Invictus

Yarima Harry da matarsa Meghan sun isa Nijeriya don halartar Wasannin Invictus

Ma'auratan, sun ziyarci kasar ta Yammacin Afirka a karon farko bisa gayyatar da sojojinta suka yi musu.
Harry da Meghan za su gana da sojojin da suka jikkata da kuma iyalansu / Hoto: AFP

Yarima Harry da matarsa, Meghan, sun isa Najeriya a ranar Juma'a, don halartar Gasar Invictus Games, wanda ya kafa don taimakawa wajen farfado da wadanda suka jikkata da marasa lafiya da kuma tsofaffin sojoji, ciki har da sojojin Nijeriya da ke yaƙi da 'yan tawaye na tsawon shekaru 14.

Ma'auratan, wadanda suka ziyarci kasar ta Yammacin Afirka a karon farko bisa gayyatar sojojinta, sun isa Abuja babban birnin kasar, da safiyar Juma'a, kamar yadda mai magana da yawun rundunar soji Birgediya Janar Tukur Gusau ya faɗa.

Harry da Meghan za su gana da sojojin da suka jikkata da kuma iyalansu a wani abin da jami'an Nijeriya suka ce na nuna goyon baya ne don inganta yanayi sojojin da jin daɗinsu.

Abidemi Marquis, daraktan wasanni a Hedkwatar Tsaron Najeriya, ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa "Wannan wasannin na Invictus yana bai wa sojojinmu damar murmurewa da dawo da walwalarsu."

Taimaka wa ga tsofaffin sojoji da suka jikkata

Harry ya yi aiki a Afganistan a matsayin ma'aikacin jirgin sama mai saukar ungulu na Apache, bayan nan ne ya ƙirƙiri Wasannin Invictus a shekarar 2014 don ba wa tsoffin sojoji da ma'aikatan da suka ji rauni damar fafatawa a wasannin motsa jiki irin na Paralympics.

Nijeriya na daga cikin ƙasashen da suka gudanar da gasar a bara.

A yayin zaman nasu za su halarci wasannin ƙwallon kwando da wasan ƙwallon raga da kuma ganawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu a Abuja da Legas da ke samun tallafi daga gare su.

Meghan za ta kuma shirya wani taron mata kan jagoranci tare da Ngozi Okonjo-Iweala, Darakta Janar na Hukumar Kasuwanci ta Duniya, a cewar mai magana da yawunsu, Charlie Gipson.

Shirin waraka

Labarin ziyarar Meghan ya burge wasu a Nijeriya, inda ake bin diddigin rayuwarta da dangantakarta da gidan Sarautar Birtaniya.

Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana Wasannin Invictus a matsayin wanda zai taimaka wajen warkewar dubban jami’anta daga firgicin da suka shiga sakamakon yaƙi da ‘yan kungiyar Boko Haram tun shekarar 2009, lokacin da suka kaddamar da hare-hare.

"Kashi 80 cikin 100 na sojojinmu da suka shiga cikin wannan shirin na farfadowa suna samun sauki (kuma) yanayin rayuwarsu na sauyawa da kyau," in ji Marquis, daraktan wasanni na soja.

"Shirin farfadowar ya ba su dama don farfaɗo da ƙimarsu, da inganta lafiyar ƙwaƙwalwarsu da hankali."

AP