Wannan shi ne harin ta'addanci mafi muni da aka kai a kasar dangane da asarar rayukan mutane a 'yan kwanakin nan, in ji kafar yada labaran kasar. / Hoto: Ministère de la Défense Nationale

Akalla sojojin kasar Benin 30 ne aka kashe a garin Banikoara da ke arewacin kasar a lokacin da wasu da ba a san ko su waye ba suka kai musu hari, kamar yadda wani jami’in sojin kasar ya bayyaba a yammacin Alhamis.

Rahotannin farko da kafafen watsa labarai suka fara ruwaitowa sun ce an kashe sojoji 28 a harin ta’addancin da aka kai ranar Laraba a Banikoara, da ke kan iyaka tsakanin Benin, Burkina Faso da Nijar.

Sai dai wani jami’in sojan kasar ta Benin da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu ta wayar tarho cewa aƙalla sojoji 30 ne suka mutu a harin, kuma sojoji sun kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’addan da ke yankin, wanda hakan ya sa aka ci galaba sosai a kan ‘yan ta’adan.

Sai dai jami’in ya ce a halin yanzu ana ci gaba da tattara bayanan hukuma kuma nan ba da jimawa ba za a fitar da sanarwa ga manema labarai domin bayar da karin bayani game da harin da kuma farmakin da sojojin suka kai.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne kafar yada labaran kasar Olofofo ta ruwaito cewa an kwashe kusan sa’o’i takwas ana musayar wuta sannan kuma maharan sun kashe tare da kona sojojin Benin 30.

Wannan shi ne harin ta'addanci mafi muni da aka kai a kasar dangane da asarar rayukan mutane a 'yan kwanakin nan, in ji kafar yada labaran kasar.

Rundunar sojojin kasar ta Benin ba ta bayyana kungiyar ta'addancin da ta kai harin ba.

Sai dai hare-haren da ake kaiwa arewacin Benin ya karu a shekarun baya-bayan nan, musamman na kungiyar ISIS (Daesh) da kungiyoyin ta'addancin al-Qaeda da ke aiki a kasashe makwabta. Yankin kan iyaka da Burkina Faso ya kasance cibiyar hare-haren.

AA